logo

HAUSA

Najeriya ta kaddamar da shirin raya kasa na shekaru hudu

2021-12-23 09:00:12 CRI

Jiya ne gwamnatin Najeriya, ta kaddamar da shirin raya kasa na tsawon shekaru hudu, da nufin aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, da sauran ayyukan raya kasa a fadin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne, ya kaddamar da shirin ci gaban kasar (NDP) wanda za a aiwatar daga shekarar 2021 zuwa 2025, yayin taron majalisar ministocin kasar na mako-mako da ya gudana a fadar shugaban kasa dake Abuja, babban birnin kasar. An tsara sabon kundin don maye gurbin tsarin farfado da tattalin arziki da bunkasuwa wato (ERGP 2017-2020) wanda ya kare a watan Disamba 2020.

Da take jawabi a yayin taron kaddamar da kundin, ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta Najeriya Zainab Ahmed, ta ce gwamnati na da burin daukar matakan da suka dace, wadanda za su sauya fasalin tattalin arziki, da yadda ake gudanar da harkokin kasuwanci na gwamnati, don inganta sabbin hanyoyin tsare-tsaren ci gaba na matsakaicin zango.(Ibrahim)