logo

HAUSA

Liu Yihua: Wasan Kongzhu na samun sabon ci gaba a zamanin yanzu a kasar Sin

2021-12-23 20:42:51 CRI

Liu Yihua: Wasan Kongzhu na samun sabon ci gaba a zamanin yanzu a kasar Sin_fororder_微信图片_20211221194609

Wasan Kongzhu yana da dogon tarihi a kasar Sin. Wasan gargajiya ne na kasar Sin, wanda ya samu shahara a tsawon shekaru fiye da 600 a kasar Sin. Ana bukatar fasahohi wajen yin wasan Kongzhu.

Liu Yihua mai shekaru 26 da haihuwa, tsohuwar daliba ce a jami’ar koyon ilmin wasannin motsa jiki ta birnin Shanghai, wadda ta gama karatu a shekarar bara, ta kuma fara aiki a wata makaranta. Yayin da take karatu a jami’a, ta yi nazari kan wasannin gargajiya na kasar Sin, kana ta koyi fasahohin wasu wasan gargajiya na kasar Sin, kamar su ‘yar igiya, da wasan Kongzhu.

Da farko dai, Liu Yihua ta koyi fasahohin ‘yar igiya a jami’a. Game da yaya ta fara koyon wasan Kongzhu, akwai wani labari mai ban sha’awa. Wato a lokacin da take karatu a digiri na biyu a jami’ar, wata abokiyar karatunta dake zaune a daki guda tare da Liu Yihua, ta yi nazari kan batun dake shafar wasan Kongzhu. Don haka, a lokacin da babu karatu, ita da Liu Yihua su kan yi wasan Kongzhu tare. Daga baya, an kafa wani kwas na musamman na koyar da fasahohin wasan Kongzhu a jami’ar, Liu Yihua da abokanta su shiga kwas din tare da fara wasan Kongzhu. Ana iya cewa, abokiyarta ta jawo Liu Yihua ta shiga wasan Kongzhu.

Bayan da ta fara koyon wasan Kongzhu, ta gano wasu alamu musamman na wasan dake bambanta da sauran wasannin gargajiya na kasar Sin. Liu Yihua ta bayyana cewa,“Na farko, a ganina wasan Kongzhu na da sauki, inda ake daukar wata igiya da wani kwanon Kongzhu, sai a yi wasan a ko ina. A yanzu, na shiga aiki, amma ina ajiye Kongzhu a cikin jaka ta. Zan yi wasan idan ina da lokaci. Na biyu kuma, ana yin amfani da kafada da wuya wajen yin wasan Kongzhu, kuma idan na yi aiki har na tsawon lokaci, zan yi wasan Kongzhu don sassauta ciwo da gajiyar kafada da wuya na.”

Liu Yihua ta ce, tana ganin wasan Kongzhu wasa ne maras wuya, kuma idan tana son koyon wata fasahar wasan mai wuya, tana iya kara kokari har ta cimma nasara. A ganinta, wasan Kongzhu wasa ne mai ban sha’awa, ba ta jin wuya ko gajiya wajen yin wasan.

Liu Yihua na ganin cewa, wasan Kongzhu ya kawo wasu canji ga aikinta da kuma zaman rayuwarta. Game da aikin, tana kokarin shigar da wasan zuwa kwas da ta koya, kuma a zaman rayuwarta, tana samun kwanciyar hankali yayin da take yin wasan Kongzhu. Liu Yihua ta bayyana cewa,“A halin yanzu, ni malama ce a wata makaranta dake birnin Shanghai. Yayin da nake aiki, ina iya koyar wa dalibai na fasahohin wasan Kongzhu. Ta haka za a kara shigar da sabon salon wasannin motsa jiki a kwas din makarantar. Kana ina son kafa kwas na musamman, don koyar da fasahohin wasan Kongzhu. Kaza lika a zaman rayuwata, yin wasan Kongzhu zai taimaka min wajen kwantar da hankali da jin dadi.”

Liu Yihua ta ce, har yanzu ba ta taba halartar gasar wasan Kongzhu ba tukuna, amma ta taba gwada fasahohin wasan Kongzhu a wasu bukukuwa. Kana ba ta halarci kowace jarrabawa, da auna kwarewarta a wasan Kongzhu ba. Amma ta ce, a jami’arta, an taba gabatar da ma’aunin matsayin fasahohin wasan Kongzhu, inda ta koyi fasahohi bisa ma’aunin don inganta fasahohinta kan wasan.

Liu Yihua: Wasan Kongzhu na samun sabon ci gaba a zamanin yanzu a kasar Sin_fororder_微信图片_20211221195243

Game da salon wasan Kongzhu, Liu Yihua ta ce, ban da damar mutum daya ya yi wasan, akwai kuma yadda mutane biyu ko mutane da yawa ke yin wasan tare. Idan mutane biyu suna yin wasan Kongzhu tare, suna iya yin wasan da gwada fasahohi iri daya, kana suna iya yin hadin gwiwa da jefawa da karbo Kongzhu a yayin wasan. Game da mutane da ke yin wasan Kongzhu tare, Liu Yihua ta bayyana cewa, a kan shigar da kide-kide da raye-raye a cikin wasan Kongzhu. Ta ce,“A ajin koyon wasan Kongzhu a jami’armu, daliban ajin su kan koyi wani shirin musamman na hadin gwiwa a kowane rabin shekara na karatu, dukkan su suna koyon fasahohi, da gwada kwarewarsu, da kuma yin hadin gwiwa tare da kide-kide da raye-raye.”

Liu Yihua ta kara da cewa, ban da raye-raye, wasan Kongzhu yana hade da wasu wasannin gargajiya na kasar Sin, kamar wasan Wushu da ‘yar igiya da sauransu. Kana ta ce ta taba kallon wani shirin da aka gwada a kasashen waje, inda aka gwada hada wasan Kongzhu da wasan kwaikwayo na dandali.

Zhan Jing, abokiyar karatun jami’a ta Liu Yihua ce, ta kuma bayyana cewa, abu mafi burgewa game da Liu Yihua shi ne, Liu Yihua ba ma kawai tana aikinta mai kyau ba ne, har ma tana yin kokari don maida aikinta mafi kyau. Ta ce wasan Kongzhu ya taimakawa Liu Yihua wajen kwantar da hankali da kara jin dadin rayuwarta. Zhan Jing ta ce,“Bayan da ta fara yin wasan Kongzhu, ta kara maida hankali ga koyon fasahohin wasan, da kara nuna sha’awar wasan. Kana ta kiyaye yin kokari wajen raya fasahohinta na wasan. Lokacin da ta fuskanci matsaloli yayin koyon fasahohin wasan, ta kan tambayi malamanmu, da tattaunawa tare da mu don warware matsalolin tare.”

Game da bunkasuwar wasan Kongzhu a kasar Sin, Liu Yihua ta ce tana yin nazari kan wannan batu a halin yanzu, ta kuma gano cewa, yanzu wasan Kongzhu ya samu karbuwa sosai a yankin Taiwan na kasar Sin, har matsayin wasan a yankin ya kai na wasan kwallon kwando, da kwallon kafa a babban yankin kasar Sin. Kana ta san cewa an kafa wasu kwas na koyar da fasahohin wasan Kongzhu a wasu jami’o’in kasashen waje. Amma ban da su, babu mutane da dama da suke sha’awar wasan Kongzhu a zamanin yanzu. Kaza lika a birnin Shanghai, yawancin mutanen da suke yin wasan tsofaffi ne. A ganin Liu Yihua, dukkan mutane, ko yara ko balagai, ko tsofaffi, suna iya yin wasan Kongzhu. Ta ce an fara shigar da wasu kwas na musamman na koyar da daliban makarantun firamare a birnin Shanghai, don sa kaimi ga yara su maida hankali ga irin wasan motsa jiki na gargajiya na kasar Sin. Liu Yihua ta ce, a wasu shekaru fiye da 10 da suka gabata, matasan kasar Sin suna son koyon fasahohi ko batutuwa daga kasashen waje. A ganinsu abubuwa na kasashen waje suna da kyau. Amma a wadannan shekaru, matasan kasar Sin suna son al’adun gargajiya na kasar Sin sosai. Ta ce “A wasu lokuta yayin da nake yin wasan Kongzhu a jami’a, akwai wasu yara ko matasa, da suke zuwa su tambaye ni game da wasan Kongzhu. Su kan ce, wannan abun gargajiya ne na kasar Sin? Babu shakka yana da kyau ssoai, suna sha’awar sa, da kuma alfahari da al’adun gargajiya na kasar Sin. Don haka, koda yake a da an daina bunkasa wasu abubuwan gargajiya na kasar Sin, amma yanzu mutanen kasarmu suna alfahari da abubuwan gargajiya na kasar Sin, suna kuma son raya su. Liu Yihua ta bayyana cewa,“Wasannin gargajiya na kasar Sin suna da kyakkyawar makoma. Koda yake mun rasa wasu damar bunkasa su a da, amma yanzu kasarmu ta samu ci gaba, muna kara alfahari da al’adunmu sosai. Za mu kara maida hankali, da nuna sha’awa ga abubuwan dake shafar al’adun gargajiya na kasar Sin.”

Liu Yihua: Wasan Kongzhu na samun sabon ci gaba a zamanin yanzu a kasar Sin

A matsayin wata malama mai koyar da wasannin motsa jiki a makaranta, Liu Yihua tana son ci gaba da bunkasa wasannin gargajiya na kasar Sin, da shigar da sabbin salon wasannin motsa jiki a cikin kwas na wasanni a makaranta, da kuma koyar da dalibai fasahohin wasannin motsa jiki iri daban daban. Tana kuma fatan ta hakan, dalibanta za su kara jin dadin rayuwarsu ta hanyar yin wasannin.

A ganin Liu Yihua, wasannin gargajiya na kasar Sin, musamman wasan Kongzhu ba lafiyar jiki kadai yake kawo mata ba, har ma ya taimake ta wajen kwantar da hankalinta. Tana jin dadin yin wasan sosai, kana tana fatan za a bunkasa wasannin gargajiya na kasar Sin, kuma karin mutane za su shiga wasannin a nan gaba. (Zainab Zhang)