logo

HAUSA

Biden ya ce zai tsayawa takarar shugaban kasa a 2024 idan yana cikin koshin lafiya

2021-12-23 10:24:16 CRI

Shugaban Amurka Joe Biden, ya fada jiya Laraba cewa, zai sake tsayawa takara a shekara ta 2024 idan har a lokacin yana cikin koshin lafiya.

Biden ya bayyana haka ne, lokacin da David Muir, mai gabatar da shiri ya tambaye shi, ko yana shirin sake tsayawa takara, a wata hira da aka watsa jiya Laraba a kafar watsa labarai ta ABC, inda shugaban ya amsa da cewa, “Eh”.

Biden ya fadawa mai gabatar da shirin cewa, “Amma ni mutumin ne mai yarda da kaddara. Kuma kaddara ta sha yin tasiri a rayuwata. Don haka, idan ina cikin koshin lafiya kamar yadda nake a halin yanzu, hakika zan sake tsayawa takara.”

Muir ya tambayi Biden, ko har yanzu yana son tsayawa takara idan abokin hamayyarsa, Donald Trump ya sake zama tsohon shugaba.

Biden ya amsa cikin dariya, "Yanzu dai kuna kokarin gwada ni." Inda ya kada baki ya ce, "Tabbas. Me ya sa ba zan yi takara da Donald Trump ba? Hakan zai kara min kaimin tsayawa takara." (Ibrahim)