logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya karbi zagaye na uku na rigakafin COVID-19

2021-12-22 09:54:08 CRI

Shugaban Najeriya ya karbi zagaye na uku na rigakafin COVID-19_fororder_尼日利亚总统-buhari

A ranar Talata shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya karbi zagaye na uku na allurar rigakafin cutar COVID-19, inda ya kasance mutum na farko da aka fara yiwa rigakafin zagaye na uku a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

Babban mai taimakawa shugaba Buhari a fannin kula da lafiya Suhayb Rafindadi, shi ne ya yi shugaban kasar allurar a fadar gwamnati dake  Abuja, a wani dan kwarya-kwaryar taro na manyan jami’an gwamnatin kasar.

Faisal Shuaib, shugaban hukumar kiwon lafiya matakin farko na kasar, ya bayyanawa taron manema labarai a Abuja cewa, shi ma mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo, da kuma wasu manyan jami’an gwamnati, da suka hada da ministan lafiya Osagie Ehanire, sun karbi zagaye na uku na rigakafin.

A cewar Shuaib, amincewar da shugabannin suka yi na karbar rigakafin zagaye na uku ya tabbatar da cewa, rigakafin cutar ta COVID-19 ba shi da wata illa.

Kawo yanzu, sama da mutane miliyan 8 ne suka karbi rigakafin COVID-19 a Najeriya, a cewar babban jami’in hukumar lafiyar kasar, ya kara da cewa, kasar ta samar da isassun alluran da za a baiwa ‘yan kasar da suka cancanta.(Ahmad)