logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijar ya gana da mashawarcin shugaban Nijar

2021-12-22 10:26:35 CRI

Jakadan Sin dake Nijar ya gana da mashawarcin shugaban Nijar_fororder_图片1

Jiya Talata, jakadan kasar Sin dake Jamhuriyar Nijar, Mista Jiang Feng, ya gana da mai baiwa shugaban Nijar shawara na musamman, mallam Garba, inda suka yi musanyar ra’ayoyi kan raya huldodin kasashen biyu.

Mallam Garba ya godewa kasar Sin matuka saboda taimakon maras sharadi da ta dade take samar mata, baya ga dadadden zumunci tsakanin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin da Jamhuriyar Nijar. Haka kuma kasashen biyu suna yin hadin-gwiwa a fannoni daban-daban, musamman ganin yadda hadin-gwiwarsu a fannin man fetur ke da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da rayuwar al’umma a Nijar. Mallam Garba ya ce, yana fatan kara azama wajen zurfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Shi ma a nasa bangaren, jakada Jiang Feng ya bayyana cewa, Nijar babbar aminiyar kasar Sin ce, kuma kasashen biyu sun dade da fahimta da baiwa juna goyon-baya a wasu muhimman batutuwan da suka shafi moriyarsu. Kasar Sin na fatan hada kai tare da Nijar, don taimakawa ga ci gaban dangantakarsu zuwa sabon matsayi. (Murtala Zhang)