logo

HAUSA

Taron Demokiradiyar da Amurka ta kira munafarci ne kawai

2021-12-22 21:47:09 CRI

A ranar 9 ga watan Disamban wannan shekra ce, kasar Amurka ta kira wani taron da ta sanya ma taken wai “Taron kolin dimokuradiyya.” A yayin bikin bude taron, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya ce, dimokuradiyya na fuskantar kalubale a fadin duniya, kuma wai dimokuradiyya na bukatar kariya.

Taron Demokiradiyar da Amurka ta kira munafarci ne kawai_fororder_211222世界21048-hoto2

Kamar yadda Emma Ashford, babbar manazarciya a hukumar Atlantic Council ta bayyana cikin wani sharhi da aka wallafa a mujallar “Foreign Policy” cewa, “Idan babu wani tsarin dimokuradiyya da ke iya aiki yadda ya kamata a cikin kasar Amurka, to, ta yaya za ta iya wanzar da dimokuradiyya tare da zama misali ga sauran kasashe?”

Demokuradiyya dai shi ne yadda jama’ar kasa ke iya gudanar da harkokinta. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, dimokuradiyya ba abin ado ba ne, abu ne da ke taimaka wa wajen daidaita matsalolin da al’umma ke fuskanta.

Taron Demokiradiyar da Amurka ta kira munafarci ne kawai_fororder_211222世界21048-hoto3

Akwai hanyoyi da dama na wanzar da dimokuradiyya a maimakon tsarin da kasashen yamma ke bi. Yadda za a tabbatar da zaman walwalar jama’a shi ne ma’auni daya kacal na tantance tsarin dimokuradiyyar wata kasa yana da kyau ko a’a. Wani abin takaici shi ne, a yayin da shugaba Biden ke lacca a kan batun dimokuradiyya, wasu a wajen hedkwatar MDD da ke birnin New York, kuma suna gudanar da zanga-zanga dauke da wani akwatin gawo da aka rubutawa “Dimokuradiyyar Amurka” a jikinsa, don gudanar da jana’izar dimokuradiyyar kasar. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)