logo

HAUSA

Masu Kishin Kasa Ne Kadai Za Su Tafiyar Da Harkokin Hong Kong

2021-12-22 17:07:51 CRI

Masu Kishin Kasa Ne Kadai Za Su Tafiyar Da Harkokin Hong Kong_fororder_1222-01

A wannan makon ne, ofishin yada labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani mai taken "Ci gaban demokuradiyya a Hong Kong, karkashin manufar ‘kasa daya amma tsarin mulki biyu’", inda aka yi bayani dalla-dalla kan tarihin demokuradiyyar Hong Kong, da matsayin gwamnatin tsakiyar kasar Sin kan yadda take goyon bayan Hong Kong, da raya tsarin demokuradiyya bisa hakikanin halin da yankin na Hong Kong ke ciki.

Yankin Hong Kong dai, ya shafe shekaru 150 karkashin mulkin kasar Birtaniya, kuma a iya tsawon wannan lokaci, ta sha hana yin gyare-gyare kan harkokin demokuradiyya a yankin, abin da ke nuna cewa, babu wani abu mai kama da tsarin demokuradiyya a Hong Kong.  Amma bayan da yankin na Hong Kong ya dawo karkashin ikon kasar Sin a shekarar 1997, a karo na farko mazauna yankin sun samu damar tafiyar da harkokinsu da kansu, karkashin manufar “kasa daya amma tsarin mulki biyu”.

Bayan daukar wasu jerin managartan matakai da mahukuntan kasar Sin suka yi game da yankin Hong Kong, ciki har da dokar tsaro da ta zaben yankin, sun taimaka matuka wajen inganta ci gaban yankin a dukkan fannoni. Na baya-bayan nan, shi ne zaben ’yan majalisar kafa doka karo na 7 da ya gudana cikin nasara.

Abubuwan da suka faru cikin shekaru 24 da suka wuce a yankin na Hong Kong sun nuna cewa, kokarin kafa tsarin demokuradiyya mai salon kasashen yammacin duniya ko ta halin kaka, ya jefa yankin cikin rudani ne kawai. Wannan ya tilastawa yankin na Hong Kong zabar raya demokuradiyyar da ta dace da yankin da ma ci gaban babban yankin kasar Sin baki daya, mai salon manufar “kasa daya amma tsarin mulki biyu” da manyan dokokin yankin, tare da barin ’yan kishin kasa su gudanar da harkokin yankin na Hong Kong bisa hakikanin halin da yankin ke ciki, bisa doka da tsari. Domin kowane tsunstu kukan gidansu yake yi.

Har kullum gwamnatin tsakiyar kasar Sin, na taimakawa bunkasuwar demorakudiyyar Hong Kong, da nuna goyon baya, da kiyaye manyan muradun mazauna Hong Kong baki daya. Don haka, duk wani yunkuri da kasashen yamma da ’yan barandansu ke yi na barnata demokuradiyyar Hong Kong, da haddasa rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arzkin yanki ba zai taba yin nasara ba.

Duk mai bibiyar abubuwan dake faruwa a yankin Hong Kong, ya san cewa, yanzu haka demokuradiyyar Hong Kong tana cikin kyakkyawar makoma. Hong Kong dai yanki ne na kasar Sin, kuma tsarin zaben Hong Kong, harkokin cikin gidan kasar Sin ne. Don haka, gwamnatin tsakiya za ta ci gaba da goyon bayan Hong Kong wajen bijiro da dukkan matakan da suka dace wajen raya dimokuradiyyar da ta dace da yankin.

Yanzu dai an kammala zaben ’yan majalisar kafa doka guda 90 a yankin musamman na Hong Kong, inda masu zabe sama da miliyan guda suka zabi masu kishin kasa, wadanda za su ja ragamar harkokin yankinsu da kansu. Don haka, masu neman amfani da matasa don tayar da fitina a yankin ta hanyar fakewa da tsarin demokiradiya ko ’yancin, bakin Alkalami ya riga ya bushe. (Ibrahim Yaya)