logo

HAUSA

Al’adun gargajiya na farkon shiga yanayin sanyi

2021-12-21 14:49:12 cri

Al’adun gargajiya na farkon shiga yanayin sanyi_fororder_1

Da misalin karfe 11:59 na daren ranar 21 ga watan Disamba, kasar Sin ta shiga ranar farko ta yanayin sanyi, wanda shi ne karo na 22 bisa kalandar noma da yanayi ta gargajiyar kasar Sin mai lokuta guda 24

Tsawon lokacin yanayin sanyi yana farawa ne daga ranar 21-23 ga watan Disamba bisa kalandar Gregorian na kowace shekara. Bisa ilmin nazarin taurari, dare ya fi rana tsayi a yankin arewa.

Bayan wannan lokacin, sai a shiga lokacin sanyi mai tsanani. Baya ga farkon shiga yanayin sanyi,haka kuma lokaci ne na biki na Sinawa. Al'adun gargajiya na farkon shiga yanayin sanyi da aka gada har ya zuwa yau, sun hada da mutunta lokuta bisa kalandar noma da yanayi ta gargajiyar kasar da al’adar Sinawa ta mutunta kakanni.Bisa al’ada ana cin dafaffiyar Dambu wato Jiao Zi a wannan rana.(Mai fassara: Bilklisu Xin)