logo

HAUSA

Wane Ne Ke Lalata Dimokuradiyyar Hong Kong?

2021-12-21 11:05:16 cri

Wane Ne Ke Lalata Dimokuradiyyar Hong Kong?_fororder_微信图片_20211221104352

JIya ne, wata kungiya mai suna "Five Eyes Alliance" wadda kasashen Amurka da Birtaniya da Canada da Australia da New Zealand suka kafa, ta fitar da sanarwar hadin gwiwa ta ministocin harkokin wajen kasar, inda suka furta kalaman rashin imani kan zaben majalisar tsara dokokin Hong Kong na kasar Sin karo na bakwai, da aka kammala yadda ya kamata. Sanarwar ta zargin zaben a matsayin "mai raunata iko da 'yanci da kuma cin gashin kan yankin Hong Kong’. Har ma ya sake yin amfani da "Sanarwar hadin gwiwa tsakanin Sin da Burtaniya" don tabo wannan batu.

A lokacin da dimokuradiyyar Hong Kong ke samun ci gaban, kungiyar " Five Eyes Alliance " ta fitar da irin wannan sanarwar da ba ta dace ba, wadda kuma ba wai kawai tana nuna fushinta saboda gazawarsu ta tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong ba, har ma ta tabbatar da cewa Amurka, Biritaniya da wasu kasashen yammacin duniya kalilan, su ne suke “karya doka” daga waje da ke kawo cikas ga ci gaban demokradiyya na Hong Kong.

Hakika, idan ana maganar dimokuradiyya da hakkin dan Adam, abin da ya kamata kasashen kungiyar “Five Eyes Alliance” su yi shi ne, su kalli kansu, su nazarci gazawarsu ta magance matsalolin da suka shafi yaki da annobar COVID-19, da mummunan adawa tsakanin jam’iyyun siyasa, da nuna wariyar launin fata da dai sauransu.

Hong Kong yanki ne na kasar Sin, kuma tsarin zaben Hong Kong, harkokin cikin gidan kasar Sin ne. Don haka, gwamnatin tsakiya za ta ci gaba da goyon bayan Hong Kong wajen daukar hanyar raya dimokuradiyya wadda ta dace da ita. Alamu na nuna cewa, akwai haske a tsarin dimokuradiyya na Hong Kong, kuma duk wani tsangwama daga kasashen waje, to tabbas ba zai yi nasara ba (Mai fassara: Bilkisu Xin)