logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu a hare-haren da aka kai arewacin Najeriya ya kai 40

2021-12-21 09:07:17 CRI

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya bayyana cewa adadin wadanda suka mutu, sakamakon hare-haren da aka kai a karshen mako a kauyukan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ya kai 40, yayin da aka sake gano wasu gawarwaki biyu a ranar Litinin.

Samuel Aruwan, ya bayyana haka ne, a cikin wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa, jami’an tsaro sun tattara gawarwaki 40 a kauyuka uku na karamar hukumar Giwa dake jihar ta Kaduna, wadanda ‘yan bindiga suka kai wa hari a tsakanin daren Asabar zuwa safiyar Lahadi.

Aruwan ya ce, idan za a iya tunawa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan Kauran Fawa, da Marke, da Riheya da ke karamar hukumar Giwa, inda aka tabbatar da mutuwar mutane 38 ya zuwa Lahadi.

Kwamishinan ya kara da cewa, gano wasu gawarwaki biyu na baya-bayan nan, ya kawo adadin wadanda suka mutu a hare-haren zuwa 40.(Ibrahim)