logo

HAUSA

Ministan wajen Sin ya takaita dangantaka tsakanin Sin da kasashen waje a 2021

2021-12-21 10:41:10 CRI

Ministan wajen Sin ya takaita dangantaka tsakanin Sin da kasashen waje a 2021_fororder_王毅

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da jawabi a gun taron karawa juna sani kan yanayin kasa da kasa, da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen ketare a shekarar 2021.

Wang Yi ya bayyana yayin da yake jawabi a wajen taron, wanda cibiyar nazarin kasa da kasa ta kasar Sin, da asusun nazarin kasa da kasa na kasar Sin suka shirya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar cewa, a cikin shekarar da ta gabata, duniya ta sha fama da annobar da har yanzu ba a shawo kanta ba, tana kuma kara sauyawa cikin sauri da ba a taba ganin irinsa ba a cikin karni, da kuma lokaci da ake fama da rikici da sauye-sauye a duniya baki daya.

Wang ya kara da cewa, yayin da ake fuskantar kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba, kasashen duniya na neman amsoshi, kuma daukacin bil-adama na bukatar zabin da ya dace. Yana mai cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka da bangare na tarihi, da ci gaban bil-adama, da daidaito a tsakanin kasa da kasa, da adalci, da kuma kasashe masu tasowa da dama.

Dangane da harkokin diflomasiyya na kasar Sin a cikin shekarar da ta gabata kuwa, babban jagorar aiki shi ne, harkokin diflomasiyya na shugabannin kasashe, babban bambanci shi ne, gina al'umma mai makoma bai daya ga daukacin bil-adama. Kuma babban batu shi ne, ba da labarin al'ummar Sinawa a duniya, da JKS. Sai dai abin da ya fi daukar hankali, shi ne sabawa da sauye-sauye yadda ya kamata, da ci gaba da kafa sabbin sakamako.

Wang Yi ya ce, yayin da annobar COVID-19 ke ci gaba da sake bulla a sassan duniya, ita kuwa kasar Sin ta gudanar da aikin diflomasiyya mai inganci na yaki da cutar COVID-19, tare da sauke nauyin da ke wuyanta, a matsauyinta na babbar kasa.(Ibrahim)