logo

HAUSA

Yarinyar dake cike da imani kan zaman rayuwarta

2021-12-21 14:42:29 cri

Girgizar kasa ta Wenchuan da ta faru ba zato ba tsammani a shekaru 13 da suka wuce, ita ce girgizar kasa mafi yin barna, kuma mafi wuyar gudanar da ayyukan ceto, wadda kuma ta shafi yankuna mafi yawa a kasar Sin. Tun bayan kafuwar sabuwar kasar, girgizar kasan ta kashe mutane kimanin dubu 80 tare da lalata rayuwar iyalai da dama. Niu Yu na daya daga cikin miliyoyin mutanen da bala’in ya shafa.

A shekara ta 2008, an binne Niu Yu 'yar shekaru 11 a karkashin baraguzan girgizar kasar na tsawon kwanaki uku, bayan da aka ceto ta, an yanke kafarta ta dama, kuma an yi mata tiyata fiye da sau 30 don ceto kafarta ta hagu. Amma, wannan yarinya ba ta taba rasa kwarin gwiwa a rayuwa ba. A yau, za mu kawo muku labarin yarinyar nan mai suna Niu Yu.

Lokacin da girgizar kasa ta Wenchuan ta auku a ranar 12 ga watan Mayun shekarar 2008, Niu Yu, wadda ke aji na biyar a makarantar firamare, tana koyon Turanci a makarantar. Ranar ce kuma ranar cikar ta shekaru 11 a duniya. Ta yi fatan hura kyandir da kuma cin waina tare da iyayenta bayan ta kammala karatu a makaranta.

Yarinyar dake cike da imani kan zaman rayuwarta_fororder_8624151f085afd9f7c8225775b66d005

Amma, a daidai wannan lokacin, fitilun da aka rataye a saman ajin sun fara rawa da karfi, kuma matakalar ginin suka rika karkadawa, malamin ya gano cewa, girgizar kasa ce ta faru. Nan da nan ya gaya wa daliban su fice cikin sauri bisa tsari. Amma an riga an makara, benaye suka karye saboda girgizar kasar, kuma gini ya danna Niu Yu.

Bayan da ta makale na tsawon kwanaki uku da dare uku, an ceto Niu Yu. Amma dukkan tantanin halittar kafar daman ta sun lalace, ta yadda dole aka yanke ta kuma aka sanya mata na karfe.

Lokacin da komai ya dawo daidai, Niu Yu ta koma makaranta, kuma ta daina rawa da ta fi so a baya. Ta kan yi kishi idan ta ga sauran ‘yan mata sanye da kaya masu kyau da gajeren siket, saboda nakasar kafarta, ita kuwa a duk tsawon shekara tana sanya da dogon wando kadai.

Amma Niu Yu ba ta yi watsi da fatanta kan makoma ba, ta kara kokari kan karatu cike da imani kan zaman rayuwa.

Saboda Niu Yu ta dade ba ta motsa jiki, kafarta ta dama ta fara shanyewa, likitan ya gaya mata cewa, idan ta ci gaba da yin haka, ba za ta iya tafiya yadda ya kamata ba, idan shekarunta na haihuwa suka kai 40.

Yarinyar dake cike da imani kan zaman rayuwarta_fororder_25a0a7a5-06bc-4beb-adc8-6eb02454ade8

A ranar 12 ga watan Mayu na shekarar 2018, wato lokaci da ta cika shekaru goma da tuna aukuwar girgizar kasar Wenchuan, an yi shirin gudanar da wasan Marathon na rabin zango a yankin. Wadanda suka halarci gasar sun kasance mutanen da suka taba fuskantar girgizar kasar Wenchuan. Niu Yu ta kuma yi rajistar halartar wasan, ta yi ta motsa jiki sosai a kowace rana, daga rabin sa'a a farko zuwa sa'o'i hudu ko biyar a karshe.

A yayin wasan, ta zage damtse wajen fallasa karayar kafarta a idanun jama'a, sannan wata kawarta ta rike ta don fara wasan.

Sau da yawa ciwon kafarta ta ya sa ta so ta janye jiki daga gasar, amma kullum akwai wata murya a cikin zuciyarta dake gaya mata cewa, dole ta yi tsayin daka. Minti goma, minti ashirin, sa'a daya,... A karshe, bayan fiye da sa'o'i hudu, Niu Yu ta kammala wasanta na Marathon na rabin zango.

Duk da ta kwanta kusan kwana uku bayan wasan, amma ba ta yi bakin ciki ba saboda ta shawo kan matsaloli a kan tunani da nakasar ta ke haifarwa.

A ranar 11 ga watan Oktoba na shekarar 2021, wani abu da ya canza rayuwar Niu Yu ya faru a wannan rana, “Makon Kaya na Shanghai” wato shahararren bikin nuna kayayyakin gayu ya gayyaci Niu Yu don halartar bikin nuna kayan zamani.

Da ta samu labarin, Niu Yu ta yi farin ciki kwarai da gaske, saboda nuna kayan zamani a dandalin ya kasance burinta ne a cikin dogon lokaci. Amma, saboda nakasarta, babu wani bikin da ya amince da irin bukatarta.

Yarinyar dake cike da imani kan zaman rayuwarta_fororder_e51e5863-458d-4f76-a449-b3df349671f4

Gaskiya, wannan dama ce mai kyau gare ta, kuma nan da nan ta karbi gayyatar da farin ciki. Daga baya kuma Niu Yu, wadda ba ta da gogewa a fagen nuna kayan gayu, ta fara koyan ilimin da ya dace game da tafiya a dandali.

Ba da dadewa ba, ranar 11 ga watan Oktoba ta zo, Niu Yu tana sanye da farar riga mai kaho da siket mai ninki-ninki, tare da sanya kyawawan lamuni a kafar ta ta dama ta karfe.

A yayin da take tafiya a dandali don nuna kayayyakin zamani, imanin da ta nuna ya burge masu kallo sosai, kuma sun yi ta tafi don nuna mata yabo.

An sanya bidiyon game da wannan biki a intanet, masu bibiyar yanar gizo sun ce, nune-nunen da Niu Yu ta yi, ya burge mu, da kuma ba mu mamaki sosai, har ma ta fi wasu shahararrun masu nuna kayan gayu, ta bayyana jajircewar nakasassu.

Niu Yu ta dauki bidiyo masu yawa iri daban daban, game da yadda take zaman rayuwa, ta kuma sanya su a yanar gizo. A cikin bidiyon, ta kan sanya fitilu masu launuka daban daban kan kafarta ta karfe, a karkashin hasken dare, kafar dama ta Niu Yu tana da kyau sosai, har ta fi ta ainihin kafa.

Wata rana, yayin da Niu Yu ke cikin motar taxi, direban ya tambaye ta cewa, me ya lalata mata kafa. Ita kuwa Niu Yu ta gaya wa direban gaskiya, direban ya dagawa Niu Yu babban yatsa don nuna yabo.

Yanzu dai Niu Yu ta saba da irin wannan rayuwar, kuma dauka da tsara gajerun bidiyoyi ya kasance muhimmin aikinta, tana da raye-raye da fara'a kuma masu amfani da yanar gizo suna sonta sosai.

Niu Yu ta cimma burinta daya bayan daya ta iyakacin kokarin da ta yi, kuma ya zama wani ma'auni ga nakasassu.