logo

HAUSA

Me yasa kasashen duniya ke rububin shiga shawarar ‘ziri daya da hanya daya’?

2021-12-20 19:11:40 CRI

Me yasa kasashen duniya ke rububin shiga shawarar ‘ziri daya da hanya daya’?_fororder_1220-1

Kamar dai yadda masu hikimar magana ke cewa, “hannu daya baya daukar jinka”. Ko shakka babu, shawarar da kasar Sin ta gabatar ta ‘ziri daya da hanya daya’, ta kasance babbar manufar raya cigaban duniya, musamman ta fannonin bunkasar tattalin arziki, samar da kayayyakin more rayuwa, da samar da guraben ayyukan yi a tsakanin alummar kasa da kasa, musamman a daidai wannan lokaci da duniya ke fama da tarin matsaloli sakamakon koma bayan tattalin arziki da duniyar ke fuskanta a sanadiyyar barkewar annobar COVID-19, da matsalar sauyin yanayi da makamantansu. Tun bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, kasashen duniya ke cigaba da yin marhabun da shawarar, musamman duba da dunbun alfanun dake tattare da ita. Kawo yanzu, yawan yarjeniyoyin “ziri daya da hanya daya” da Sin ta kulla da kasashen waje sun zarce 200. Ko shakka babu, wannan gagarumar nasara ce ga cigaban duniya. Kamar yadda mai magana da yawun hukumar kula da aikin gyare-gyare da raya kasa ta kasar Sin Meng Wei, ta bayyana a karshen wannan mako cewa, Sin ta kulla yarjejeniyoyi karkarshin shawarar “ziri daya da hanya daya” da gwamnatocin Afrika ta tsakiya, da Guinea Bissau, da Eritrea, da Burkina Faso, da Sao Tome da Principe, da sauran kasashen Afrika da dama. Kuma ya zuwa yanzu, kasar Sin ta kulla irin wadannan yarjejeniyoyi fiye da 200 da kasashe 145, da kungiyoyin kasa da kasa 32. Madam Meng ta ce, a kwanakin baya an kira taro karo na farko tsakanin Sin da AU, kan daidaita ayyukan dake shafar shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, inda bangarorin biyu suka tattauna kan batun yakar COVID-19, da samar da hatsi, da makamashi, da zuba jari, da samar da muhimman ababen more rayuwa, da makamantansu, matakin da ya kara zurfafa hadin kansu. Ban da wanann kuma, mahalarta taron sun rattaba hannu kan ‘takardar fahimtar juna, tsakanin hukumar yin gyare-gyare da raya kasa ta kasar Sin, da kwamitin AU, game da karfafa hadin gwiwar bangarorin 2 karkashin shawarar ‘ziri daya da hanya daya’. Dama dai masu hikimar magana na cewa, “Juma’a mai kyau tun daga Laraba ake ganeta”, kuma a bisa dukkan alamu shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ tana taka gagarumar rawar a zo a gani wajen fidda jaki daga duma a daidai lokacin da duniya ke neman dauki sakamakon manyan kalubalolin dake barazana ga cigaban duniyar.(Ahmad Fagam)