logo

HAUSA

Sharhi:Tabbatar da ci gaba shi ne tushen hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka

2021-12-20 13:48:53 CRI

Tabbatar da ci gaba shi ne tushen hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka_fororder_ae0cd2faf0e7148f147fb39f270ed898

Noman tushen tattalin arziki.

A yayin bikin kaddamar da taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, wanda aka kammala kwanan baya a kasar Senegal, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da shirye-shiryen hadin gwiwa guda tara, a tsakanin kasarsa da kasashen Afirka, ciki har da shirin saukaka fatara da tallafawa manoma, kuma a kwanan nan, aka kaddamar da rukuni na farko na cibiyoyin hadin-gwiwar Sin da Afirka na gwaji da samar da horo wajen musanyar fasahohin aikin gona na zamani, wanda ya kasance muhimmin mataki na aiwatar da shirin.

Alkawari kaya ne. Yau sama da makwanni biyu kacal ke nan da kaddamar da taron, amma ga shi har an fara tabbatar da sakamakon da aka cimma a gun taron sannu a hankali, wanda ya shaida yadda kasar Sin ke cika alkawuranta a kullum, da ma yadda hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ke samar da hakikanin nasarori.

Idan mun yi nazari a kan matsalolin da kasashen Afirka ke fuskanta ta fannonin siyasa da tattalin arziki, da zamantakewar al’umma da dai sauran fannoni, lallai za mu gano cewa, rashin ci gabansu shi ne ainihin dalilin da ya haifar da hakan. Don haka, a yayin da kasar Sin take aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka, kullum tana mai da hankali a kan alakanta ci gaban kanta da na kasashen Afirka, tare da daukar hakikanin matakai na taimakawa kasashen Afirka samun ci gabansu.

A hakika, shirye-shiryen hadin gwiwa guda tara, da kasar Sin ta gabatar a gun taron ministoci karo na takwas na dandalin FOCAC, sun mai da hankali a kan batun ci gaba, wadanda suka shafi fannonin kandagarkin cutar Covid-19, da saukaka fatara, da tallafawa manoma wadanda ke da muhimmanci ga ci gaban kasashen Afirka, wadanda kuma suka daidaita matsalolin da kasashen Afirka ke fuskanta ta fannin ci gabansu.

In an dauki misali da cibiyoyin hadin gwiwar da aka kaddamar a wannan karo, wadanda suke lardunan Hainan, da Jiangsu, da Sichuan, da kuma Shaanxi na kasar Sin, wadanda kuma suka yi fice ta fannoni daban daban, ciki har da noman amfanin gona a yanayin zafi, da noman shinkafa, da kiwon albarkatun ruwa, da yaki da kwararowar hamada da sauransu, wadanda kuma suke biyan bukatun kasashen Afirka daban daban ta fannin raya ayyukan gona.

Marigayi Deng Xiaoping, wanda ya tsara aikin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare na kasar Sin, ya taba bayyana cewa, “Samun ci gaba shi ne abu mafi muhimmanci.” A game da shakku da ma bakin fenti da ake shafawa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, ci gaban da kasashen Afirka suka samu sakamakon hadin gwiwarsu da kasar Sin ya kasance martani mafi karfi.

Yanzu makwanni biyu ke nan da kammala taron, kuma har wasu kasashen Afirka biyar, ciki har da Somaliya da Gambiya da Mozambique da Nijar gami da Kamaru, suka riga suka samu alluran riga-kafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samar musu. Haka kuma, kwamitin tsara ka’idojin biyan harajin kwastam na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya sanar da cewa, kasar za ta soke harajin kwastam kan kaso 98 bisa dari na hajojin wasu kasashen dake fama da matsanancin rashin ci gaba, a wani kokari na fadada shigo da kayayyaki daga kasashen Afirka, da more damammakin kasuwanci tare da kasashen.

Ba shakka, samun ci gaba ba abu ne mai sauki ba, sai dai bisa yadda kasashen Afirka da Sin ke tallafawa juna, don rungumar makomarsu ta bai daya, tabbas ne akwai makoma mai haske a gare su. (Lubabatu)