logo

HAUSA

Jihar Xinjiang tana kan hanyar samun bunkasuwa da wadata

2021-12-20 20:49:07 CRI

Game da daftarin dakile tilastawa ‘yan Uygur yin aiki tilas, wanda majalissun dokokin kasar Amurka suka zartas, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, koda yake ‘yan siyasar Amurka suna da niyyar tada hargitsi, amma ba za a iya hana jihar Xinjiang samun ci gaba da bunkasuwa da wadata ba.

Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, game da tilastawa mutane su yi aiki, ya dace Amurka ta yi la’akari da kanta. Ya ce ya zuwa yanzu, akwai yara kimanin dubu 500 da suke yin aikin gona a kasar Amurka. A cikin shekaru 5 da suka gabata, yawan mutanen da aka sayar da su a kasar Amurka don tilasa musu yin aiki a kowace shekara ya kai dubu 100.

Ya ce Sin ta kalubalanci mutanen da aka maida su matsayin wakilan kasar Amurka, da su sa lura ga harkokin kasarsu da kansu. (Zainab)