logo

HAUSA

Kamfanin Nanchang ya fara ayyukan share fage na gina sabuwar madatsar ruwa ta Harare

2021-12-17 10:01:56 CMG

Kamfanin Nanchang ya fara ayyukan share fage na gina sabuwar madatsar ruwa ta Harare_fororder_211217-Saminu1

Kamfanin Nanchang na kasar Sin, ya fara ayyukan share fage, na gina sabuwar madatsar ruwa ta Kunzvi, a gundumar Goromonzi na lardin gabashin Mashonaland dake kasar Zimbabwe, domin samar da isasshen ruwa ga birnin Harare.

Ana sa ran aikin wanda zai lashe kudi har dalar Amurka miliyan 109, zai kawar da matsalar karancin ruwa da birnin Harare ke fama da shi, inda birnin ke dogaro ga cibiyoyin samar da ruwa 4, cikin su har da 2 da ke kunshe da gurbataccen ruwa.

Tuni dai shugabannin al’umma na yankin suka fara jinjinawa wannan muhimmin aiki, wanda suka yi imanin zai inganta rayuwar al’umma, musamman kasancewarsa zai kyautata ayyukan noman rani a yankin.

Jami’an ma’aikatar albarkatun ruwa na kasar sun ce, kamfanin da zai gudanar da aiki, tare da hukumomi masu ruwa da tsaki, sun gana da shugabannin gargajiya a yankin, inda aka gudanar da al’adu na share fagen gudanar aikin.

Da yake tsokaci game da aikin, kansilan mazabar Goromonzi ta 12 Kondwakuenda Magaya, ya ce baya ga samar da guraben ayyukan yi na wucin gadi, aikin zai kuma haifar da guraben ayyuka na dindindin, yayin da ruwan da Dam din zai samar zai yi amfani ga manoman rani.

Kaza lika a cewarsa, Dam din zai ba da damar farfado da gandayen daji, da bunkasa sassan tattalin arzikin mazauna yankin, da karin guraben ayyukan yi gare su.   (Saminu)

Saminu