logo

HAUSA

NATO da EU sun yi kira da a kai zuciya nesa game da takaddamar Rasha da Ukraine

2021-12-17 11:28:54 CMG

NATO da EU sun yi kira da a kai zuciya nesa game da takaddamar Rasha da Ukraine_fororder_211217-Saminu3

Kungiyar tsaro ta NATO, ta yi kira da a kai zuciya nesa game da takaddamar dake wakana tsakanin Rasha da Ukraine, da ma yadda hakan ke kara haifar da zaman dar-dar a kan iyakar gabashin Ukraine. Kungiyar ta kuma sha alwashin tallafawa Ukraine wajen kare yankunan ta, tare da gabatarwa Rasha damar hawa teburin shawara.

Da yake karin haske game da hakan, bayan kammala wata ganawa da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy a birnin Brussels, babban sakataren kungiyar Jens Stoltenberg, ya ce suna kira ga Rasha da ta komawa matakan diflomasiyya, ta kaucewa rura wutar tashin hankali, kana ta martaba ikon mulkin kai da tsaron yankunan Ukraine. Mr. Stoltenberg ya yi gargadin cewa, duk wani mataki na muzgunawa Ukraine zai gamu da mummunan martani.

A nasu bangaren, shugabannin kungiyar tarayyar turai ta EU, sun tattauna, tare da tsara yiwuwar kakabawa Rasha takunkumi, muddin ta ki amincewa da rage adadin dakarun sojin ta a kan iyakar Ukraine.

Shi kuwa shugaba Vladimir Putin na Rasha, cewa ya yi akwai bukatar gaggauta fara tattaunawa, kan batutuwa da suka shafi ainihin yarjeniyoyin kasa da kasa masu nasaba da fadada dakarun NATO a gabashin kan iyaka, da adawar da kasar sa ke yi ga jibge makamai a yankuna makwaftan Rasha, musamman ma kasar Ukraine.  (Saminu)

Saminu