Kokarin Amurka na tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ba zai yi nasara ba
2021-12-17 21:48:11 CRI
Jiya ne, majalisar dattijan Amurka ta amince da dokar da ta kira wai "Dokar rigakafin tilasta wa 'yan kabilar Uyghur aikin tilas," wadda ta haramta shigo da kayayyakin da aka samar a yankin Xinjiang cikin kasuwannin Amurka, bisa dalili na wai “aikin tilas”. Wannan shi ne yadda wasu 'yan siyasar Amurka ke yin magudin siyasa, da cin zarafi a fannin tattalin arziki karkashin tutar wai kare hakkin dan Adam, matakin da ya kara bayyana munanan aniyarsu ta dakile ci gaban jihar Xinjiang, da ci gaba da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin.
Shin akwai "aikin tilas" a jihar Xinjiang? Mutanen yankin ne za su iya gaskata wannan batu. A wani taron manema labarai na baya-bayan nan da aka kira, jama’a da yawa a jihar Xinjiang, sun ba da labari game da yadda suka samu rayuwa mai dadi ta hanyar aiki. Ana iya ganin cewa, ko aiki a kusa da gida ko fita waje, hanya ce da jama'ar jihar Xinjiang za su yi rayuwa mai dadi, kuma wannan ya zama ruwan dare a dukkan kasashen duniya, amma ‘yan sisayar Amurka sun mayar da shi tamkar wani ruwan dagwalo da suke zubawa kasar Sin..
Duk wasu karairayi da magudin siyasa, ba za su iya kawar da ci gaban da jihar Xinjiang ta samu ba, ballantana a dakatar da ci gaban da ake samu a jihar Xinjiang.