logo

HAUSA

DRC ta ayyana kawo karshen annobar Ebola

2021-12-17 10:14:20 CMG

DRC ta ayyana kawo karshen annobar Ebola_fororder_211217-Ahmad1

A jiya Alhamis hukumomin lafiyar jamhuriyar demokaradiyyar Kongo sun ayyana kawo karshen annobar Ebola a hukumance wadda ta barke a baya bayan nan, wato karo na biyu da annobar ta barke a shekarar 2021.

A jimlace, an samu rahotannin barkewar cutar guda 11, an tabbatar da takwas daga cikin adadin, yayin da uku babu tabbaci, wanda ya hada da hasarar rayuka shida, an samu rahoton barkewar cutar ne a ranar 8 ga watan Oktoba a lardin Kivu dake shiyyar arewa maso gabashin DRC. Wannan shi ne karo na 13 da aka samu barkewar annobar kuma a wannan yankin ne aka samu barkewar annobar a shekarar 2018 wacce ta shafe tsawon shekaru biyu.

A cewar ministan lafiyar kasar Kongo DRC Jean-Jacques Mbungani, kwarewar da tawagar jami’an lafiyar kasar da abokan huldarsu na kasa da kasa suka samu wajen tinkarar annobar, ya taimaka wajen cimma nasarar dakile annobar cikin watanni biyu kacal bayan samun rahoton bullarta.

Daraktan hukumar lafiyar ta duniya WHO na shiyyar Afrika, Matshidiso Moeti, ya ce, tsananta bin diddigin cutar, da shigar da al’ummun yankin yaki da cutar, da yin riga-kafi a yankunan da lamarin ya shafa, da kuma daukar matakan gaggawa wajen jiyyar masu dauke da cutar sun taimaka matuka wajen cimma nasarar dakile annobar a shiyyar.(Ahmad)

Ahmad