logo

HAUSA

Asusun LLF zai samar da kudade domin aikin kare muhallin halittu a kasashen Afirka 2

2021-12-17 10:33:03 CMG

Asusun LLF zai samar da kudade domin aikin kare muhallin halittu a kasashen Afirka 2_fororder_211217-Saminu2

Asusun “Legacy Landscapes” ko LLF a takaice, ya shirya samar da kudade, domin kare wasu gandayen daji masu kunshe da mabanbantan halittu a kasashen Congo da Zimbabwe.

Asusun kasa da kasa na LLF, zai gudanar da aikin ne karkashin jagorancin ma’aikatar hadin gwiwar raya tattalin arziki da samar da ci gaba na kasar Jamus, da kuma bankunan samar da ci gaba na kasashen biyu.

Wata sanarwa da aka fitar ta ce, Asusun LLF na gudanar da ayyukan sa ne karkashin hadin gwiwar gwamnatoci da sassa masu zaman kan su, yana kuma samar da kudaden ba da kariya ga mabanbantan halittu a sassan gandayen daji.

Gandun dajin Odzala-Kokoua na kasar Congo, da na Gonarezhou dake kasar Zimbabwe ne za su ci gajiyar tallafin na wannan karo. Bisa tsarin aikin, gandayen dajin biyu za su rika samun kudi har dalar Amurka miliyan daya a duk shekara, har tsawon shekaru a kalla 15 masu zuwa.  (Saminu)

Saminu