“Ido ba mudu ba ya san kima”
2021-12-16 16:54:19 cri
Tun bayan kammala taron da Amurka ta yiwa lakabi da na “kare dimokaradiyya”, hankula ke kara karkata ga manufarta ta shirya taron, da kuma irin sakamakon da taron ya haifar.
Masharhanta da dama dai sun ga baike Amurka, game da kiran taron kare salon dimokaradiyya, a gabar da ita kan ta a cikin gida, take ci gaba da fuskantar tarin matsaloli na zamantakewa, da tsarin gudanar da gwamnati. Alal misali, cikin manyan matsalolin da kowa ke iya hange, dake ciwa Amurka tuwo a kwarya, akwai batun yawan harbe-harben bindiga na “kan mai uwa da wabi”, wanda a shekarar nan ta 2021 kadai, aka samu irin su har 652. Yayin da adadin Amurkawa da ‘yan sanda suka harbe a shekarar ya kai mutum 925.
Rahotanni sun ce adadin bakaken fata ‘yan Amurka da ‘yan sanda suka yiwa kisan gilla, ya ninka na takwarorin su fararen fata sama da sau biyu, duk da cewa adadin bakaken fatar kasar bai wuce kaso 13 bisa dari na jimillar al’ummun kasar ba!
A bangaren amfani da miyagun kwayoyi kuwa, adadin Amurkawa masu kananan shekaru dake shiga wannan mummunar al’ada na kara yawa, a gabar da gibin dake tsakanin mawadatan kasar da talakawa ke kara fadada, don haka ne ma wasu ke ganin dimokaradiyyar Amurka, na yiwa masu wadata ne kadai gata, ta yadda suke “cin karen su ba babbaka”, sauran ‘yan kasa kuma ko oho!
Kari kan hakan, a baya bayan nan, rahotanni sun tabbatar da cewa, adadin wadanda suka rasu sakamakon harbuwa da cutar COVID-19 a Amurka ya zarce mutum 800,000, yayin da kasar ta shige gaba wajen yawan wadanda suka harbu da cutar a duk fadin duniya, don haka abun tambaya a nan shi ne, anya kuwa kasar da ta gaza wajen ceton rayukan al’ummarta, ta cancanci zama mai kare dimokaradiyya? Tun da dai ai dimokaradiyyar salon mulki ne na al’umma domin cin gajiyar al’umma.
Idan kuma shi kan sa batun tsarin zabe ake yi, a Amurka, sanin kowa ne masu wadata ne ke amfani da dukiyoyi wajen juya akalar siyasa, da tsayar da ‘yan takara, da mara baya ga jam’iyyu. Idan kuwa bukatar su ba ta biya ba, akan ga yadda suke kokarin hargitsa tsarin zaben kasar baki daya, kamar dai yadda aka gani yayin da gungun magoya bayan tsohon shugaban Amurka Donald Trump suka afkawa ginin majalissar dokokin kasar na Capitol, a gab da sanar da sakamakon zaben da ya nuna rashin nasarar sa, lamarin da ya haifar da rasuwar mutane 5, tare da jikkata 140.
Bahaushe kan ce, “Ido ba mudu ba amma ya san kima”, don haka ba abun da ya dace ga Amurka, illa maida hankali ga warware tarin matsalolin dake gabanta, kafin ta samu kimar zama mai kare dimokaradiyya!