logo

HAUSA

Umar Tijjani Abdullahi: Ina son yin amfani da ilimin da na samu a kasar Sin don inganta abubuwa a gida Najeriya

2021-12-16 16:59:57 CRI

Umar Tijjani Abdullahi: Ina son yin amfani da ilimin da na samu a kasar Sin don inganta abubuwa a gida Najeriya_fororder_微信图片_20211215214600

Umar Tijjani Abdullahi, dan jihar Kano dake tarayyar Najeriya ne, wanda ya taba yin karatu a fannin injiniya na gine-gine a wata jami’a dake birnin Shenyang na kasar Sin, daga shekara ta 2015 zuwa ta 2019.

A zantawar sa da Murtala Zhang, malam Umar ya bayyana cewa, akwai bambancin yanayin karatu tsakanin gida Najeriya da kasar Sin, kuma yana fatan yin amfani da ilimin da ya samu a Sin don inganta abubuwa a Najeriya.

A karshe malam Umar ya yi kira ga daliban Najeriya, da suke karatu a kasar Sin, da su dage wajen yin karatu, don a nan gaba za su iya samun damar bautawa kasarsu. (Murtala Zhang)