logo

HAUSA

Sin: An kammala dukkan ayyuka yayin da kwanaki 50 suka rage a bude gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing

2021-12-16 19:54:12 CRI

Sin: An kammala dukkan ayyuka yayin da kwanaki 50 suka rage a bude gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing_fororder_微信图片_20211216195335

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a Alhamis din nan cewa, yau kwanaki 50 cif suka rage a bude gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi na Beijing, kuma a halin yanzu, kusan an kammala dukkan ayyukan shirya gasar.

Wang Wenbin ya bayyana hakan ne, yayin da yake amsa tambayar da wani dan jarida ya yi masa, yana mai cewa, ”kamar yadda na sani, 'yan wasa daga ko'ina a duniya, suna Allah-Allah su halarci gasar a kasar Sin. Ya kara da cewa, ‘yan wasa suna amfani da kwanaki 50 da suka rage wajen shiga gasar gwaji, da kara samun horo. Don haka, muna yi wa 'yan wasa daga dukkan kasashe fatan kafa sabbin bajinta a wasannin Olympics na lokacin sanyi, za kuma mu yaba da rawar da 'yan wasa daga ko ina cikin duniya suka taka.”