logo

HAUSA

Kyan alkawari cikawa

2021-12-16 20:46:55 CRI

Kyan alkawari cikawa_fororder_src=http___06imgmini_eastday_com_mobile_20180905_20180905003430_2519d96f4f6f5c940b873a6b3a1ddf74_1_jpeg&refer=http___06imgmini_eastday

A yayin bikin kaddamar da taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wanda aka kammala kwanan baya a kasar Senegal, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar sa za ta kafa wasu cibiyoyin hadin-gwiwar Sin da Afirka na gwaji da samar da horo wajen musanyar fasahohin aikin gona na zamani. A jiya Laraba ne aka kaddamar da irin wadannan cibiyoyi a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yau Alhamis cewa, kafa irin wadannan cibiyoyi wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka a fannin rage talauci da samar da alheri ga manoma, al’amarin da kuma ya zama daya daga cikin wasu muhimman ayyuka tara da kasar Sin ta sanar za ta yi don inganta hadin-gwiwarta da Afirka a wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC.

Wang ya jaddada cewa, kyan alkawari cikawa. Yanzu makwanni biyu ke nan da kammala taron, inda wasu kasashen Afirka biyar, ciki har da Somaliya da Gambiya da Mozambique da Nijar gami da Kamaru, suka riga suka samu alluran riga-kafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samar musu. Haka kuma kwamitin tsara ka’idojin biyan harajin kwastam na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya sanar da cewa, kasar za ta soke harajin kwastam kan kaso 98 bisa dari na hajojin wasu kasashen dake fama da matsanancin rashin ci gaba, a wani kokari na fadada shigo da kayayyaki daga kasashen Afirka, da more damammakin kasuwanci tare da kasashen. (Murtala Zhang)