Taron G7 Ya bar Jaki Yana dukan Teki
2021-12-15 16:52:53 CRI
A wannan makon ne, kungiyar kasashen G7 ta gudanar da taronta a birnin Liverpool na kasar Burtaniya. Sai dai sabanin abin da ya kamata kungiyar ta tattauna game da abubuwa dake addabar duniya a halin da ake ciki da zakulo hanyoyin magance su, sai ta kauce hanya tana shiga shoro ba shuna, ta hanyar tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin. Wannan ya sa bangaren kasar Sin ya nuna adawa da yadda kungiyar ta G7 take tsoma baki a harkokin cikin gidanta, da neman bata sunan kasar, da ma cutar da muradun kasar ta Sin.
Rahotanni sun bayyana cewa, sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Elizabeth Truss wadda kasarta ke shugabancin kungiyar a wannan karo, ta bayyana cikin wata sanarwa yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar cewa, bangarorin sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi kasar Sin, ciki har da zaman lafiyar Hong Kong, da Xinjiang, da tekun gabashi da na kudancin kasar Sin, da kuma mashigin tekun Taiwan da sauransu. Wannan ba shi ne ainihin abin da ya kamata kasashen kungiyar su tattauna ba.
Sai dai, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin kan wadannan batutuwa bai sauya ba. Don haka, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba don kare halastattun muradun ta bisa doka.
Alkaluma na nuna cewa, jimillar al'ummar Amurka da Biritaniya ta kai kusan kashi 5% na al'ummar duniya, kuma su ne kasashe mafi ci gaban tattalin arziki da fasahar likitanci a duniya, sai dai duk wannan ci gaba, al’ummomin kasashen su ba su gani a kasa ba, wai ana biki a gidansu kare, inda masu kamuwa da cutar COVID-19 da kuma wadanda ke mutuwa sakamakon cutar, ya kai kusan kashi 23% da 18% bi da bi a duniya baki daya.
A don haka, maimakon bata lokaci suna shiga hurumin wasu kasashe, da batun demikoiradiya da ’yancin dan-Adam marasa tushe, kamata ya yi kasashen Amurka da Biritaniya da sauran wasu kasashe, su kare hakkin jama’arsu na rayuwa da lafiya, tare da yin aiki tukuru don hana karin asarar rayukan jama’a sakamakon annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar sassan duniya.
Wannan ya nuna a fili yadda kungiyar G7 baki daya, ta bar Jaki tana dukan Teki, inda ta kauce daga muhimman abubuwan da ya kamata ta tattaunawa a wannan lokaci da duniya ke fama da manyan kalubaloli da ya dace a kai ga samo bakin zaren warware su. (Ibrahim Yaya)