logo

HAUSA

Sin: Idan Amurka ta nace kan shirinta, hakika Sin za ta mayar da martani

2021-12-15 21:01:52 CRI

Sin: Idan Amurka ta nace kan shirinta, hakika Sin za ta mayar da martani_fororder_aa18972bd40735fa4fdc3bebfb159bba0f240805

Dangane da amincewa da kudurin doka mai alaka da jihar Xinjiang da Amurka ta yi, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labarai na yau da kullum a Larabar nan cewa, kasar Sin na adawa da tsoma bakin majalisar dokokin Amurka kan harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da batutuwa masu alaka da jihar Xinjiang.

A jiya ne majalisar wakilan Amurka, ta zartar da shirin dokar da ta kira wai, dokar hana aikin tilas ta Uygur, wadda ta samu amincewar majalisar dattawa da ta wakilan Amurka, inda aka mika ta ga shugaban kasa don ya sa mata hannu, bayan an gama tattaunawa a majalisar Dattawa.

Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, "Kasancewar abin da aka kira wai ‘kisan kare dangi’ da ‘aikin tilas’ a jihar Xinjiang, karya ce da aka shafe shekaru ana yi, amma ta samu gindin zama a tsarin siyasar Amurka. Don haka, kasar Sin za ta tabbatar da kare tsaron kasa da moriyar ci gabanta. Haka kuma idan har Amurka ta nace wajen gabatar da kudirin da abin ya shafa, ko shakka babu kasar Sin za ta mayar da martani.”