logo

HAUSA

Kamaru ta karbi tallafin rigakafin COVID-19 miliyan 1 daga Sin

2021-12-15 10:31:30 CMG

Kamaru ta karbi tallafin rigakafin COVID-19 miliyan 1 daga Sin_fororder_211215-S1Kamaru

A jiya Talata ne tallafin rigakafi miliyan daya, na kamfanin Sinopharm da kasar Sin ta samarwa kasar Kamaru, ya isa filin jirgin saman Nsimalen dake birnin Yaounde.

Jami’in lura da fannin tattalin arziki da cinikayya na ofishin jakadancin Sin dake Kamaru Guo Jianjun, da babban sakataren ofishin ayyukan rigakafi na Kamaru Shalom Tchokfe Ndoula, sun halarci bikin karbar rigakafin.

Da yake tsokaci kan hakan, Guo Jianjun ya ce yayin dandali na 8 na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da aka kammala kwanakin baya a kasar Senegal, Sin ta alkawarta samarwa kasashen Afirka da tallafin rigakafin COVID-19 har biliyan daya. Kuma ko shakka babu, karkashin tsarin ayyukan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin kiwon lafiya, da yaki da annobar COVID-19, sassan biyu za su cimma manyan nasarori.

A nasa tsokaci kuwa, Mr. Shalom Tchokfe Ndoula cewa ya yi, rigakafin COVID-19 shi ne kan gaba, wajen shawo kan wannan annoba, da ma ganin bayan ta baki daya. To sai dai kuma karancin rigakafin na cikin abubuwan da ke ciwa Kamaru tuwo a kwarya, kuma samun rigakafi miliyan daya daga Sin, zai taimakawa kasar fadada yiwa al’ummun ta rigakafi.

Ya ce wannan tallafi ya kara zurfafa kawancen da sassan biyu suka dade da kullawa a fannin kiwon lafiya, da ma dadaddiyar abotar kasashen biyu.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne, kasar Sin ta mikawa Kamaru kason farko na tallafin rigakafin samfurin kamfanin Sinopharm guda 200,000.    (Saminu)

Saminu