logo

HAUSA

Sin ta ba da gudunmawar tallafin abinci ga Uganda

2021-12-15 10:47:31 CMG

Sin ta ba da gudunmawar tallafin abinci ga Uganda_fororder_211215-A2-Uganda

A ranar Talata kasar Sin ta bayar da gudunmawar tallafin abinci wanda darajarsa ta kai dala miliyan 2 ga shirin samar da abinci na MDD, WFP, don ciyar da abincin ga yara ‘yan makaranta a yankin Karamoja dake shiyyar arewa maso gabashin kasar Uganda.

A watan Fabrairu, kasar Sin da shirin WFP, sun sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya don samar da sama da ton 3,000 na tallafin abinci wanda darajarsa ta kai dala miliyan 2 ga kasar Uganda. Ana sa ran tallafin abincin zai amfanawa sama da mutane 120,000 a makarantu 300 a yankin na Karamoja.

Abdirahman Meygag, jami’in kula da shirin WFP a kasar Uganda, ya ce gudunmawar da kasar Sin ta samar yana da matukar muhimmanci wajen taimakawa yaran don su samu damar koyon ilimi duk da kasancewar makarantun kasar sun jima a kulle sakamakon annobar COVID-19.

A bisa ga shirin na WFP, ana sayen abinci ne daga manoman kasar da nufin bunkasa tattalin arzikin cikin gidan kasar.(Ahmad)

Ahmad