logo

HAUSA

Ba wanda zai illata gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing

2021-12-14 10:31:45 CRI

Ba wanda zai illata gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing_fororder_微信图片_20211214103116

Kwanan baya, wasu kasashe ciki har da Amurka da Birtaniya, sun yi ikirarin cewa, ba za su tura jami’ansu don halartar gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing ba. Amma sai dai kuma da ma can Sin ba ta gayyaci jami’an wadannan kasashe ba, don haka abin da suka yi, ya zama wasan siyasa nasu kawai. Kaza lika ko za su halarta ko ba za su halarta, ba zai illata gasar ba ko kadan.

Gasar Olympics ta lokacin hunturu ta kasance wani gagarumin biki ne ga ’yan wasanni da masu sha’awar gasannin kankara, ba dandalin ’yan siyasa ba. Wadannan kasashe su kadai na son mayar da gasar wasan siyasa, kuma saura kasashe suna matukar sa ran a gudanar da gasar cikin nasara. A wani bangare na daban, ’yan wasanni sun shirya tsaf domin shiga gasar.

A halin yanzu, cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa a duniya, kuma wasu yankuna na sake fuskantar rikice-rikice. Saboda haka, gasar da za a yi ta wuce bikin wasanni kawai, domin kuwa za ta zama wani kyakkyawan fata ga Bil Adama ne ta fuskar hadin kai, da sada zumunci da zaman lafiya. Wasu kasashe ciki hada Amurka da Birtaniya, ba za su wakilci wannan gasa ba. Kasashen duniya na da imanin cewa, bayan kusan kwanaki 50, ba shakka gasar za ta gudana cikin gagarumar nasara. (Amina Xu)