logo

HAUSA

Wata tankar gas ta haddasa gobara a garin Onitsha na jihar Anambra

2021-12-14 10:16:12 CRI

Wata tankar gas ta haddasa gobara a garin Onitsha na jihar Anambra_fororder_1214-saminu-2

Rahotanni daga jihar Anambra dake kudancin Najeriya, na cewa wata tankar iskar gas da ta yi bindiga a garin Onitsha na tsakiyar jihar, ta haddasa gobara, wadda ta kone motoci da dama a daren ranar Lahadi.

A cewar hukumar kashe gobara ta jihar, gobarar ta lakume gidaje da dama, tare da wasu gidajen man fetur 2, da kuma wani garejin gyaran motoci, to sai dai kuma ba a samu rahoton asarar rayuka ko jikkatar mutane ba.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, kwamandan hukumar kare hadurra reshen jihar ta Anambra Adeoye Irelewuyi, ya ce tuni jami’an hukumar suka killace wurin da lamarin ya auku, tare da karkata ababen hawa dake bin yankin zuwa wasu tituna na daban. Ya kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulan su, tare da yin hakuri da tasirin yanayin da ake ciki.  (Saminu)