logo

HAUSA

Kauracewa gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, siyasa ce kawai

2021-12-14 09:04:54 CRI

Yayin da kasar Sin ta kammala dukkan shirye-shiryen karbar bakuncin gasar wasanin Olympics ta lokacin huturu a shekarar 2022, sai ga shi kasar Amurka da ’yan kanzaginta sun ce, jami’ansu ba za su halarci gasar ba. Amma jama’a daga sassa daban-daban na duniya na cewa, kauracewa halartar gasar Olympics ta Beijing ta shekarar 2022 da jami’an wasu kasashe za su yi, siyasa ce kawai. Sun kuma nuna kwarin gwiwa cewa, duk da wannan makircin, sama da 'yan wasa 15,000 sun nuna aniyarsu ta shiga gasar a shekara mai zuwa. Kuma kasar Sin, za ta gabatar da wani gagarumin biki a shekara mai zuwa.

Kauracewa gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, siyasa ce kawai_fororder_211215世界21047-hoto4

Shi ma shugaban girmamawa na kungiyar wasan kwallon raga ta duniya (FIVB) Wei Jizhong ya bayyana cewa, ko jami'an gwamnatocin wasu kasashen yammacin duniya sun halarci gasar Olympics ta lokacin sanyi ta 2022 da birnin Beijing zai karbi bakunci ko a’a, da kyar hakan ya yi wani tasiri a gasar . Yana mai cewa, Amurka ta yi hakan ne, da niyyar kawo cikas da kuma lalata wasannin na 2022, amma burinsu ba zai cika ba. Ya ce a cikin 'yan shekarun nan, wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaru na yammacin duniya, sun nemi bata sunan kasar Sin, lamarin da ya rikitar da al'ummar kasashen waje da dama. Amma a cewarsa, kamar yadda gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi ta 2008 ta yi, wasannin lokacin sanyi na 2022 ma, za su ba da wata dama ga jama'ar yammacin duniya, su fahimci hakikanin kasar Sin. (Saminu, Ibrahim, Sanusi Chen)