logo

HAUSA

Jami’an tsaro a Kamaru sun gudanar da atisayen yaki da ta’addanci a filin wasa na Omnisport a kudu maso yammacin kasar

2021-12-14 10:51:22 CRI

Jami’an tsaro a Kamaru sun gudanar da atisayen yaki da ta’addanci a filin wasa na Omnisport a kudu maso yammacin kasar_fororder_1214-saminu-4

Gabanin bude gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka da za a kaddamar a wata mai zuwa a Kamaru, jami’an tsaron kasar sun gudanar da wasu jerin atisayen yaki da ta’addanci, a yankin kudu maso yammacin kasar.

An gudanar da atisayen ne a jiya Litinin, a filin wasa na Limbe Omnisport, dake yankin da mazaunansa ke amfani da Turancin Ingilishi, a wani mataki na shirin ko ta kwana, wanda zai baiwa jami’an tsaron damar dakile duk wani hari na ababen fashewa ko garkuwa da mutane.

Atisayen tsaron dai, ya hallara sojoji, da ’yan sanda, da jami’an kashe gobara, da na jinya da dai sauransu. Ya kuma gudana a filin wasa na Omnisport, inda za a gudanar da wasannin rukunin F, mai kunshe da kungiyoyin kwallon kafar kasashen Tunisia, da Mali, da Mauritania da Gambia.

Yayin atisayen, an gwada yadda ’yan ta’adda ka iya ta da abun fashewa a filin wasa, da yadda ake iya yin garkuwa da mutane, tare da yunkurin guduwa da su, kafin jami’an tsaron su samu nasarar harbe ’yan ta’addan na gwaji.

Da yake tsokaci kan haka, jami’in rundunar sojojin kasar Ignatius Akuni, ya ce "Atisayen da suka gudanar, wani gwaji ne na karfin dakarun tsaron kasar, wanda ke tabbatarwa daukacin wadanda za su halarci gasar ta AFCON cewa, an shirya kare rayukan su yadda ya kamata "

Za dai a buga gasar cin kofin kwallon kafar Afirka ne a kasar Kamaru, tsakanin ranekun 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairun shekarar dake tafe.   (Saminu)