logo

HAUSA

Taron dimokaradiyyar Amurka ya kara tona asirin kasar

2021-12-14 10:08:38 CRI

Taron dimokaradiyyar Amurka ya kara tona asirin kasar_fororder_1214-saminu-1

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce taron dimokaradiyya da Amurka ta kira kwanan nan, ya kara fallasa asirin ta na kasancewa mai yiwa salon mulkin dimokaradiyya zagon kasa mai makon mai ba shi kariya.

Wang, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce mutane kalilan ne suka kalli bidiyon taron da Amurka ta kira da sunan kare dimokaradiyya ta yanar gizo, yayin da dumbin mutane suka kalli bidiyon yadda sojojin Amurka ke shiga wasu kasashe tare da hallaka fararen hula, wadanda ba su ji, ba su gani ba.

Jami’in ya kara da cewa, a yanzu duniya ba ta bukatar rarraba kasashe zuwa masu bin dimokaradiyya da wadanda ba sa bin tsarin, bisa wani mizani da wata kasa guda ta tsara, kuma duniya ba ta bukatar nuna kyama da danniya, ko kakaba takunkumi, da nuna karfin soji kan kasashe da yankuna da sunan dimokaradiyya.   (Saminu)