logo

HAUSA

An gano nau’in Omicron na cutar COVID-19 a Ghana

2021-12-14 10:36:56 CRI

An gano nau’in Omicron na cutar COVID-19 a Ghana_fororder_1214-saminu-3

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Ghana ko GHS a takaice, ta tabbatar da samun rukunin mutane na farko da suka harbu da nau’in Omicron na cutar COVID-19 a kasar.

Da yake karin haske game da hakan ta kafar talabijin din kasar, babban daraktan ma’aikatar Patrick Kuma-Aboagye, ya ce an gano karin mutane 7 da suka harbu da cutar ta hanyar gudanar da gwaji, inda jimillar masu dauke da ita a kasar ta karu zuwa mutane 41. Mr. Kuma-Aboagye ya kara da cewa, har yanzu nau’in cutar na Delta ne mafi yawa a Ghana.

Yayin da ake shirye shiryen fara shagulgulan karshen shekara, mahukunta a Ghana na ci gaba da tsaurara matakan kandagarkin bazuwar annobar, inda a yanzu mutanen da suka karbi cikakkun alluran rigakafin COVID-19 ne kadai ake baiwa izinin shiga kasar.   (Saminu)