logo

HAUSA

Idan rana ta fito tafin hannu ba zai iya rufe ta ba

2021-12-13 15:41:53 CRI

Idan rana ta fito tafin hannu ba zai iya rufe ta ba_fororder_1

Shin da gaske ‘yan kasa ne ke da hurumin auna sahihancin gwamnatinsu? Shin ko demokaradiyya zance ne na fatar baki? Ko kuma batun nan ne da malam Bahaushe kan ce, “in gani a kasa wai ana biki a gidan su kare”. Ko shaka babu, “ruwan da ya doke ka shi ne ruwa,” in ji masu hikimar zance. Tun bayan kammala taron da Amurka ta kira a makon jiya na “shugabannin demokaradiyya,” za mu iya cewa, “ya bar baya da kura”. Yayin da wasu ke ganin kwarmata bayanai game da aron salon demokaradiyyar wata kasa guda daya tilo shi ne ci gaba, wasu kuwa suna ganin baiken hakan. A mahanga ta masana da masu fashin baki kan al’amurran zamantakewa suna ganin cewa, hakikanin ma’anar demokaradiyya shi ne, shugabanci na na-gari, da kokarin gudanar da sahihin jagoranci don kyautata jin dadin rayuwar al’ummar kasa, da gina cigaban kasar, da saukaka rayuwar jama’ar kasa musamman masu karamin karfi, da samar da zaman lafiya da tsaro da makamantansu.

Game da wannan batu, masharhanta sun yi tsokaci kan yadda suke ganin irin ma’anar da kasar Sin ta baiwa demokaradiyya. Kamar yadda wani mai sharhi kan al’amurra na kasar Uganda ya ce, tsarin shugabancin kasar Sin wata shaida ce dake tabbatar da cewa manufofin bunkasa ci gaba na cikin gidan kasar suna aiki yadda ya kamata, sabanin salon demokaradiyyar da kasashen yammacin duniya ke amfani da shi wanda ke jaddada manufar “wani bangare guda shi ne ya fi kowanne." Allawi Ssemanda, babban daraktan cibiyar nazarin cigaba ta Development Watch Center, ya bayyana a karshen makon jiya cewa, "kasar Sin ta baiwa duniya tabbaci cewa tsarin shugabancinta yana aiki. An fidda miliyoyin mutane daga kangin talauci, kuma mutane na cin gajiyar shirin zaman lafiya da tsaron kasar, da ’yancin zaman rayuwar al’ummar kasa, kana da sauran hakkokin al’umma wadanda su ne hakikanin ma’anar demokaradiyya. A cewar masanin, al’ummar duniya sun ga yadda tsarin shugabancin kasar Sin ya warware matsalolin da ’yan kasar suke muradin ganin an warware su, wadanda su ne muhimman burikan duk wata gwamnatin da take da manufar gina al’ummarta. Ya kara da cewa, har ma wasu hukumomin kasa da kasa da dama sun bayyana ra’ayoyinsu game da yadda al’ummar Sinawa suke matukar nuna goyon baya da kuma amincewa da gwamnatinsu. Mista Ssemanda ya ce mutanen kasa ne kadai ke da ikon yanke hukunci game da ko gwamnatinsu ta demokaradiyya ce ko a’a, amma ba wasu gwamnatocin kasashen ketare ba. Ko shakka babu, lokaci ya yi da ya kamata hankalin mai yankar kaba ya koma gari. (Ahmad Fagam)