logo

HAUSA

Li Keqiang ya gana da shugaban bankin duniya

2021-12-13 21:26:48 CRI

Li Keqiang ya gana da shugaban bankin duniya_fororder_4ec2d5628535e5ddcbc89ae5b77936e6cf1b6268

Yau ne, firaministan kasar Li Keqiang ya gana da shugaban bankin duniya David Malpass ta kafar bidiyo. 

Yayin ganawar, Li Keqiang ya ce, ba mu dade da kiran taron kolin tattalin arziki ba. Kuma a shekara mai zuwa, za mu mayar da hankali wajen martaba manufar kiyaye ci gaban tattalin arziki ba tare da wata matsala ba. Ya ce, a yayin da ake fuskantar sabon matsin lamba, muna iya cimma manyan manufofi da ayyukan da aka sanya a gaba a shekara. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da bankin duniya, wajen bayar da kudade da ilmi, kuma tana tallafawa shawarwarin kara karfin jari na kungiyar raya kasa ta kasa(IDA) karo na 20, da daukar kwararan matakai don tallafawa tsarin kasancewar bangarori da dama da ci gaban duniya baki daya.

A nasa bangare kuwa, Malpass ya yi magana mai kyau game da yadda tattalin arzikin kasar Sin ke samun ci gaba akai-akai. Ya kuma gode wa kasar Sin bisa ga yadda ta goyi goyon kara jari ga kungiyar raya kasa da kasa, kana yana fatan ci gaba da yin hadin gwiwa mai dorewa, da ma karfafa hulda da kasar Sin.