logo

HAUSA

Shugaban AU ya yi kira da a goyi bayan shirin samar da alluran rigakafi da magunguna a Afirka

2021-12-13 20:16:02 CRI

Shugaban AU ya yi kira da a goyi bayan shirin samar da alluran rigakafi da magunguna a Afirka_fororder_1113133511850983470

Hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi kira da a tallafa wa shirye-shiryen Afirka, na samar da muhimman magunguna da alluran rigakafin fiye da na COVID-19, domin hakan shi ne mafarin tabbatar da lafiyar duniya.

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta AU, Moussa Faki Mahamat ya bayyana hakan ne a taron kula da alluran rigakafi da harkokin kiwon lafiya na duniya na zaman ministocin harkokin waje da raya kasa na kungiyar G7.

Dangane da batun isar da alluran rigakafin kuwa, shugaban hukumar ta AU ya yi nuni da cewa, an samu jinkiri a nahiyar Afirka, idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya, game da batun odar alluran a kasuwa da kuma wadanda aka yi alkawari karkashin shirin COVAX

Ya kara da cewa, nahiyar Afirka mai yawan al'umma biliyan 1.3, ita ce ke da kusan kashi 14 cikin 100 na al'ummar duniya, amma tana samar da kasa da kashi 0.1 cikin 100 na allurar rigakafi a duniya, a don haka, ya jaddada bukatar kara karfin nahiyar ta Afirka.