logo

HAUSA

Shugaban Afirka ta kudu ya kamu da cutar COVID-19

2021-12-13 09:44:54 CRI

Shugaban Afirka ta kudu ya kamu da cutar COVID-19_fororder_1213-south Africa-Saminu

Shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, na ci gaba da samun kulawar jami’an lafiya, bayan da ya killace kansa a birnin Cape Town, sakamakon harbuwa da cutar COVID-19.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Ramaphosa ya fara jin alamun cutar ne marasa tsanani, bayan da ya halarci bikin binne gawar tsohon mataimakin shugaban kasar FW de Klerk a birnin Cape Town.

Wata sanarwar da fadar gwamnatin Afirka ta kudu ta fitar a jiya Lahadi, ta nuna cewa, shugaban ya karbi cikakkun rigakafin COVID-19. A halin da ake ciki kuma, ya mika ragamar ayyukan hukuma ga mataimakinsa David Mabuza, wanda zai jagoranci ayyukan gwamnatin a tsawon makon nan.

A baya bayan nan shugaba Ramaphosa, ya kammala ziyarar kasashen yammacin Afirka 4, da suka hada da Najeriya, da Kwadebuwa, da Ghana da Senegal. To sai dai kuma, fadar shugaban kasar Afirka ta kudun ta ce an yiwa shugaba Ramaphosa da ’yan takwagarsa gwajin COVID-19, a dukkanin kasashen da ya ziyarta. Kaza lika gwajin da aka yi masa lokacin da ya sauka a birnin Johannesburg a ranar 8 ga watan nan, bayan kammala baraguron, ya nuna ba ya dauke da cutar.   (Saminu)