logo

HAUSA

Yawan GDP na kowane mutum a kasar Sin a shekarar 2021 zai kai dala dubu 12

2021-12-13 11:38:55 CRI

Yawan GDP na kowane mutum a kasar Sin a shekarar 2021 zai kai dala dubu 12_fororder_1019-1

Mataimakin shugaban ofishin kwamitin kula da kudi na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin Han Wenxiu, ya bayyana a gun taron shekara-shekara na tattalin arzikin kasar Sin daga shekarar 2021 zuwa 2022 da aka gudanar a kwanakin baya cewa, bunkasuwar tattalin arzikin Sin da yanayin magance yaduwar cutar COVID-19 a kasar, sun kai matsayin koli a duniya a shekarar 2021, inda ake sa ran cewa, yawan GDPn kasar Sin a wannan shekara zai karu da kashi 8 cikin dari. Han Wenxiu ya bayyana cewa,“A yanzu haka wasu hukumomi da masana suna sa ran cewa, yawan GDP na kasar Sin zai karu da kashi 8 cikin dari, inda yawansa zai kai Yuan triliyan 110, yayin da kuma yawan GDP na kowane mutum a kasar Sin a shekarar zai kai dala dubu 12, wanda yake kusa da matsayin samun kudin shiga mafi girma da bankin duniya ya tsaida ma’auni a fannin.”

Han Wenxiu ya kara da cewa, a shekarar 2021, a yayin da ake tinkarar cutar COVID-19, yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashen waje ya karu cikin sauri, inda yawansu bisa adadin cinikin duniya ya kai matsayin koli a tarihi.

Kaza lika jiragen kasa dake sufuri tsakanin Sin da Turai, sun samar da goyon baya, na tabbatar da samar da kayayyakin yau da kullum, da yaki da cutar COVID-19, da kiyaye farashin kaya da ake amfani da su a duniya. (Zainab)