logo

HAUSA

Zimbabwe na matukar goyon bayan gasar Olympics ta lokacin hunturu dake tafe a birnin Beijing

2021-12-13 09:52:48 CRI

Zimbabwe na matukar goyon bayan gasar Olympics ta lokacin hunturu dake tafe a birnin Beijing_fororder_1213-Zimbabwe-Saminu

Ministar ma’aikatar watsa labarai da hidimomin yada bayanai ta Zimbabwe Monica Mutsvangwa, ta ce gwamnatin kasar tana matukar goyon bayan gasar Olympics ta lokacin hunturu da birnin Beijing zai karbi bakunci a shekara mai zuwa, tana kuma adawa da yunkurin wasu kasashen yamma na siyasantar da batun gasar.

Monica Mutsvangwa, wadda ta yi wannan tsokaci a ranar Asabar, ta ce ko kadan, bai dace a siyasantar da batun wasannin ba. Kuma Zimbabwe na yiwa kasar Sin fatan alheri, da fatan nasarar gudanar da wannan muhimmiyar gasa, wadda ke tafe a gabar da kasashe da dama ke fama da bazuwar cutar COVID-19. Jami’ar ta ce tana da imani game da ikon kasar Sin na shawo kan wannan annoba.

Har ila yau, jami’ar ta ce gasar Olympics din dake tafe, ta mutane ne da suka samu horo, wadanda za su baje kolin fasahohin su yadda ya kamata ga dukkanin duniya, kuma duniya za ta nishadantu daga shirye shiryen talabijin da za a nuna game da gasar.   (Saminu)