logo

HAUSA

Kasashen gabashin Afirka hudu sun hada gwiwar yaki da dagwalon robobi

2021-12-12 17:22:38 CRI

Kasashen gabashin Afirka hudu sun hada gwiwar yaki da dagwalon robobi_fororder_bf096b63f6246b608b26eac6b192e048500fa2c3

Kasashe hudu na gabashin Afrika da suka hada da Tanzania, Kenya, Uganda da Rwanda sun hada gwiwa domin yaki da dattin robobi dake gurbata muhalli a shiyyar.

Ana Le Rocha, babbar daraktar shirin Nipe Fagio, ta ce kasashen hudu sun yanke shawarar fara gangamin raba al’ummar yankin gabashin Afrika daga robobin da ake amfani dasu sau guda a jefar da su domin zaburar da al’ummar shiyyar game da muhimmancin kaucewa amfani da robobi sau daya kawai.

Nipe Fagio da yaren Kiswahili, ma’anarsa da Turanci shi ne 'Give me the Broom', wato ba ni tsintsiya. Wata kungiya ce ta wayar da kan al’umma wanda ta mayar da hankali wajen fadakar da jama’a muhimmancin shiga aikin tabbatar da samun cigaba mai dorewa a Tanzania.

Le Rocha, ta fadawa taron manema labarai a Dodoma, babban birnin kasar Tanzanian cewa, an fara shirin ne ta hanyar gamayyar hadin gwiwar wasu kungiyoyi hudu, ciki har da Center for Environment Justice and Development (CEJAD), Global Initiative for Environment and Reconciliation (GER), da Bio Vision Africa (BiVA) da kuma Nipe Fagio.

Kasashen gabashin Afrika sun haramta amfani da robobin da ake amfani da su sau daya yayin da Rwanda ta samu gagarumar nasara a shirin, inda kasar Kenya ta sha alwashin zartar da hukunci mai tsanani ga wadanda suka gaza bin dokar.(Ahmad)