logo

HAUSA

An samu alluran riga-kafin Covid-19 masu yawa da suka lalace a Najeriya

2021-12-12 16:36:28 CRI

An samu alluran riga-kafin Covid-19 masu yawa da suka lalace a Najeriya_fororder_6939092646770262050 (1)

Rahoton kafar yada labarai na BBC na ranar 8 ga wata ya bayyana cewa, sama da alluran riga-kafin Covid-19 miliyan 1 sun lalace a Najeriya. Ma’aikatar lafiyar tarayyar Najeriyar ta tabbatar da lamarin inda ta bayyana cewa, mafi yawan alluran riga-kafin sun jima a ajiye wadanda kasashen Turai suka bayar dasu gudunmawa kuma wa’adin amfaninsu ya kusa karewa a lokacin da suka isa Najeriya.

An ce, riga-kafin da suka lalace na kamfanin AstraZeneca ne. A wannan rana kuma, wata sanarwar da ministan lafiya na kasar ya sanyawa hannu ta tabbatar da labarin, sai dai sanarwar bata fayyace adadi da kuma kamfanin alluran riga-kafin da suka lalace ba.

Sanarwar tace a baya bayan nan kasashe da dama galibi kasashen Turai sun bayar da gudunmawar riga-kafin Covid-19, inda suka bayar da alluran kyauta karkashin shirin rabon riga-kafi na (COVAX) da kuma shirin asusun sayen riga-kafi na Afirka. Koda yake, wadannan gudunmawar da aka samar abin a yi maraba da su ne kuma an yi farin ciki da hakan, sai dai yadda matsalar take shi ne, wasu daga cikin wadannan alluran watanni kadan ne suka rage kafin cikar wa’adin aikinsu. Idan aka kwashe adadin kwanakin da suka shafe wajen yin jigilarsu, da rarraba su har zuwa wuraren da za a yi wa mutane riga-kafin, lokacin amfani da su yayi matukar kankanta, kuma wasu daga cikin alluran ‘yan makonni kadan ne suka rage kafin cikar wa’adin aikinsu.

Sanarwar tace, samar da gudunmawar riga-kafin Covid-19 wadanda suke da gajeren lokacin amfani da su, ko kuma wadanda suka yi kusa lalacewa ya haifar da damuwa a tsakanin al’ummun kasa da kasa. Ya zuwa yanzu, Najeriya ta riga tayi amfani da galibin riga-kafin Covid-19 masu gajeren lokacin amfani dasu sama da miliyan 10 gabanin cikar wa’adin amfani da su. Sannan ta kwashe wadanda suka lalace ta zubar da su.(Ahmad)