logo

HAUSA

Masani: Tsarin shugabancin Sin ya ba da tabbacin bunkasuwar kasar

2021-12-11 15:39:15 CMG

Masani: Tsarin shugabancin Sin ya ba da tabbacin bunkasuwar kasar_fororder_1211-uganda-analyst-Ahmad

Wani mai sharhi kan al’amurra na kasar Uganda yace, tsarin shugabancin kasar Sin wata shaida ce dake tabbatar da cewa manufofin bunkasa cigaba na cikin gidan kasar suna aiki yadda ya kamata, sabanin salon demokaradiyyar da kasashen yammacin duniya ke amfani da shi wanda ke jaddada manufar “wani bangare guda shi ne yafi kowanne."

Allawi Ssemanda, babban daraktan cibiyar nazarin cigaba ta Development Watch Center, ya bayyana a yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua kwanan nan cewa, “Kasar Sin ta tabbatar mana cewa tsarin shugabancinta yana aiki. An fidda mutane daga talauci, kuma mutane na cin gajiyar tsaro, da ‘yanci da sauran hakkokin al’umma wadanda su ne hakikanin ma’anar demokaradiyya”.

Yace, “Dukkanmu mun ga yadda tsarin shugabancin kasar Sin ya warware matsalolin da ‘yan kasar suke son a warwaresu, wadanda su ne muhimman burikan duk wata gwamnatin da take da manufa." Ya kara da cewa, “Ba abin mamaki ba ne ganin yadda wasu hukumomin kasa da kasa, dake bayyana ra’ayoyinsu ciki har da wasu daga kasar Amurka dake nuna cewa al’ummar Sinawa suna matukar nuna goyon baya da kuma amincewa da gwamnatinsu."

Ya ce mutanen kasa ne ke da ikon yanke hukunci game da ko gwamnatinsu ta demokaradiyya ce ko a’a, amma ba wasu gwamnatocin kasashen ketare ba.(Ahmad)

Ahmad