logo

HAUSA

Kakakin ma’aikatar wajen Sin ya yi tsokaci kan “Taron kolin shugabannin demokaradiyya” da Amurka ta kira

2021-12-11 19:53:02 CRI

A yau Asabar 11 ga wata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cikin wani jawabi game da abin da aka kira wai “Taron kolin shugabannin demokaradiyya” wanda Amurka ta shirya, taron wanda aka kira wai “taron koli" ya shata layi kan wata manufa, don yin amfani da shi a matsayin wani makamin siyasa, wajen yakar tsarin demokaradiyya ta hanyar fakewar da demokaradiyyar karya. Ana haifar da rarrabuwar kai da yin fito-na-fito, da kokarin kawar da kai daga rikicin cikin gida, da nufin tabbatar da Amurka ta yiwa duniya kaka gida, da kokarin lalata tsarin kasa da kasa karkashin hakikanin dokokin MDD da tsarin doka da odar kasa da kasa. Matakin Amurkar ya ci karo da tsarin da duniya ta saba amfani da shi bisa al’ada a tarihi, kana ya gamu da mummunar adawa daga al’ummun kasa da kasa.(Ahmad)