logo

HAUSA

Manufofin raya tattalin arzikin Sin na dogon lokaci ba za su sauya ba

2021-12-11 20:11:45 CRI

Manufofin raya tattalin arzikin Sin na dogon lokaci ba za su sauya ba_fororder_中国经济

Kwamitin tsakiya na JKS ya gudanar da taron raya tattalin arziki a Beijing tsakanin 8 zuwa 10 ga watan Disamba. Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron, inda ya gabatar da muhimmin jawabi. Taron ya yi nuni da cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfi, kuma muhimman manufofin kyautata tattalin arzikin kasar na dogon lokaci ba za su taba canzawa ba. A shekarar 2022, kasar Sin za ta aiwatar da dukkan manyan dabarun hadin gwiwar raya ci gaban kasar domin daga matsayin ci gaba na gabashi, tsakiya, yammaci da kuma arewa maso gabashin kasar. Baki daya ana fatan za a farfado da yankunan karkara da inganta sabbin manufofin gina ingantaccen ci gaba a garuruwa.(Ahmad)