Yan wasan barkwanci sun baje hajarsu yayin taron demokaradiyyar Amurka
2021-12-11 20:49:08 CRI
Taron da aka kira wai “taron kolin demokaradiyya" wanda Amurka ta jagoranta ya kammala a ranar 10 ga wata. Mai tayar da tarzoma a yankin Hong Kong, Luo Guancong, da “wakiliyar gwamnati” ta Taiwan, Tang Feng, sun gabatar da wani abu mai kama da wasan kwaikwayo a wajen taron, inda suka karawa wasan armashi a gaban al’ummun kasa da kasa. Taron da aka kira wai “taron kolin demokaradiyya" makamin siyasa ne wanda Amurka ke amfani da shi don yiwa demokaradiyya kafar ungulu ta hanyar fakewa da demokaradiyya, da haifar da baraka, da yin fito-na-fito, da tabbatar da manufar Amurka na yin mulkin danniya. Babu wanda zai dauki batun da muhimmanci. Ba shi da wani sakamako face hasara.(Ahmad)