logo

HAUSA

An gudanar da taron dandalin tunawa da cika shekaru 20 da zaman Sin mambar WTO

2021-12-11 20:28:13 CRI

An gudanar da taron dandalin tunawa da cika shekaru 20 da zaman Sin mambar WTO_fororder_wto

A ranar 10 ga watan Disamba, wakilin dindindin na kasar Sin a kungiyar kasuwanci ta duniya WTO da sakatariyar gudanarwar WTO, sun shirya taron hadin gwiwa, don tunawa da cika shekaru 20 da kasancewar kasar Sin a matsayin mambar WTO" a birnin Geneva, na kasar Switzerland. Taron dandalin wanda aka gudanar ta kafar bidiyo mai taken “shekaru 20 da kasancewar kasar Sin a kungiyar WTO: Hadin kai da ci gaba". Jakada Li Chenggang, zaunannen wakilin kasar Sin a kungiyar WTO, da kuma babbar daraktar kungiyar WTO, Ngozi Okonjo Iweala, sun halarci kaddamar da bikin tare da gabatar da muhimman jawabai. Okonjo Iweala, ta bayyana kyakkyawan fata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tsarin cudanyar kasuwanci na bangarori daban daban.(Ahmad)