logo

HAUSA

Mahalarta taron demokaradiyya: Kasashen Afrika na da ‘yancin zabar salon shugabancinsu

2021-12-11 16:06:12 CMG

Mahalarta taron demokaradiyya: Kasashen Afrika na da ‘yancin zabar salon shugabancinsu_fororder_1211-Democracy-Afirka-Ahmad

Masana, wakilan gwamnatoci, da jami’an diflomasiyya sun ce, ya kamata a kyale kasashen Afrika su tsara salon shugabancinsu na cikin gida maimakon kakaba musu salon demokaradiyyar kasashen yamma wanda bai haifar musu da wani kyakkyawan sakamako ba a tsawon shekaru da dama, sun bayyana hakan ne a yayin halartar taron tattaunawa kan demokaradiyya a ranar Juma’a.

A yayin bude taron mai taken, "Kawar da demokaradiyyar yammacin duniya a Afrika", Okello Oryem, ministan harkokin wajen kasar Uganda, ya ce, ya kamata a bar mutanen Afrika su yanke hukunci kan salon demokaradiyyar da ya fi dacewa da su.

Ministan ya bayyana wajen taron na rabin wuni cewa, “Batun bin salon demokaradiyya daya a matsayin mafi dacewa ga kowa ba zai taba biyan muradun al’umma ba, kuma yana da muhimmanci a auna tsarin demokaradiyyar da zai dace da yanayin al’umma da kuma tsarin kowace kasa."

Akwai bukatar a mutunta ‘yancin da kowace kasa ke da shi na tafiyar da ikon kasar da yankunanta. Bai kamata kasashe masu karfin fada aji su dinga yanke hukunci ba, su zartar ko kuma su kakaba tsarinsu ko irin  salonsu wanda ba lallai ne ya dace da yanayin sauran kasashe ba," ya kara da cewa, ana iya aron salon demokaradiyya ne kadai bisa ga yadda zai biya muradun al’umma yadda ya kamata.(Ahmad)

Ahmad