logo

HAUSA

Sin ta shirya taron bita kan shawarar bunkasa cigaban duniya tare da wakilan MDD

2021-12-10 10:36:27 CRI

Sin ta shirya taron bita kan shawarar bunkasa cigaban duniya tare da wakilan MDD_fororder_211210-Ahmad 2-GDI

Jiya Alhamis, kasar Sin ta shirya taron karawa juna sani tare da wakilan hukumomin MDD wadanda suke zaune a nan kasar Sin domin tattauna shawarar hadin gwiwar bunkasa ci gaban duniya wato (GDI), don cimma nasarar gaggauta aiwatar da ajandar samar da ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030.

Taron bitar na hadin gwiwa ne tsakanin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, da ofishin jami’in kula da shirin raya ci gaba na MDD dake kasar Sin, taron ya samu halartar wakilai 20 daga hukumomin MDD daban daban dake kasar.

Shawarar GDI, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da ita, shawara ce dake da burin taimakawa ci gaban kasashe masu tasowa, da daga matsayin farfadowar tattalin arzikin duniya bayan kawo karshen annoba, da kuma bunkasa ci gaban hadin gwiwar kasa da kasa, kamar yadda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu, ya bayyana a wajen taron.

Wakilan da suka halarci taron, sun yaba da nasarorin da kasar Sin ta cimma wajen aiwatar da ajandar cigaba mai dorewa nan da shekarar 2030, kana sun yi maraba da shawarar ta GDI wadda Xi ya gabatar.

Sun yi tsokaci cewa, shawarar GDI za ta kara kaimin daga matsayin dabarun bunkasa ci gaban kasa da kasa, kana sun yi alkwarin goyon hayan aiwatar da shawarar ta GDI ta hanyar kyakkyawan amfani da albarkatun da ake da su, da karfafa hadin gwiwa, da yin cudanya da juna. (Ahmad Fagam)