logo

HAUSA

Abin dariya ne yadda Amurka ta kira “Taron Kolin Dimokuradiyya”

2021-12-10 21:25:24 CRI

Abin dariya ne yadda Amurka ta kira “Taron Kolin Dimokuradiyya”_fororder_微信图片_20211210210942

Jama’a, shin yaya kuke fahimtar Dimokuradiyya?

A jiya ne Amurka ta kira wani taron da ta sanya ma taken wai “Taron kolin dimokuradiyya.” A gun bikin bude taron, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya ce, dimokuradiyya na fuskantar kalubale a fadin duniya, kuma cewa ya yi dimokuradiyya na bukatar mai ba ta kariya.

Lallai wannan abun dariya ne, yadda kasar da ke fama da munanan matsaloli a gida tare da haifar da tashe-tashen hankali ga sauran kasashen duniya, take yi wa sauran kasashen duniya lacca a kan batun dimokuradiyya, ba tare da fahimtar cewa, ita ce ta haifar da mummunan misali ga sauran kasashe a fannin wanzar da dimokuradiyya ba.

Abin dariya ne yadda Amurka ta kira “Taron Kolin Dimokuradiyya”_fororder_20211208131845243

Kamar dai yadda Emma Ashford, babbar manazarciya a hukumar Atlantic Council ta bayyana cikin wani rubutunta da aka wallafa a mujallar “Foreign Policy” cewa, “Idan kusan babu wani tsarin dimokuradiyya da ke iya aiki yadda ya kamata a cikin kasar Amurka, to, ta yaya za ta iya wanzar da dimokuradiyya tare da zama misali ga sauran kasashe?”  Jaridar Premium Times ta kasar Nijeriya ita ma ta wallafa sharhi, inda ta yi nuni da cewa, bayan da kasashen Afirka suka samu ‘yancin kansu, kasashen yamma sun tilasta musu aikin “shimfida dimokuradiyya”, in ba haka ba, lallai za su daina samar musu gudummawa, matakin da ya sa gyare-gyaren tattalin arzikin kasashen Afirka sun amfani kasashen yamma, har ma kasashen Afirka suka rasa iko kan wasu fannonin tattalin arzikinsu, gwamnatocin kasashen Afirka ma sun rasa abin da za su iya dogara a kai, wajen tabbatar da dimokuradiyya da ma jin dadin al’ummunsu.

Abin dariya ne kuma, yadda aka gudanar da taro da sunan dimokuradiyya amma ba tare da sauraron ra’ayoyin gamayyar kasa da kasa, da ma sauran hukumomin duniya ba, har ma ta saka sama da rabi na kasashen duniya cikin jerin kasashen da ba sa da dimokuradiyya bisa ma’aunin da ita kanta ta tsara.

A hakika, hakan nuna fin karfi ne, wanda ya saba wa manufar dimokuradiyya. Don haka ma, gidan talabijin na kasar Afirka ta kudu, ya wallafa wani bayani a shafinsa na yanar gizo dake cewa, kasashe da dama ba su samu goron gayyatar zuwa “Taron kolin dimokuradiyya” ba, goron gayyatar da ya kasance tamkar nau’in takardar nuna amincewa, wato Amurka na neman nuna cewa, amincewar da ta nuna har ta fi taron muhimmanci, matakin da ya sa kasashe mahalarta taron da Amurkar ta zaba za su halarci wani taron da sam ba shi da ma’ana.”

Abin dariya ne yadda Amurka ta kira “Taron Kolin Dimokuradiyya”_fororder_微信图片_20211210210956

Abin dariya ne kuma, yadda aka gudanar da taron da sunan dimokuradiyya amma ba tare da nufin wanzar da dimokuradiyya ba. An lura da cewa, kasashen Rasha da Hungaria da suke kiyaye hulda mai kyau da kasar Sin, ba sa cikin jerin “kasashe masu dimokuradiyya” da aka gayyata, a yayin da kasar Lithuania wadda matsayinta bai kai na Hungaria ba a jerin kasashen da kasashen yamma suka fitar ta fannin kiyaye dimokuradiyya ta samu gayyata, kawai sabo da rawar gani da ta taka kwanan baya wajen nuna kin jinin kasar Sin. Lallai taron dai ba na dimokuradiyya ba ne, kawai mataki ne Amurka ta dauka don kulla kawance a duniya, da ma kiyaye matsayinta na kasa mafi fada a ji, kuma ba wani abu zai kawo ba illa haifar da sabani da kiyayya a tsakanin kasashen duniya. Kamar dai yadda ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce, ainihin dalilin taron shi ne tamkar “yaki” da Amurka ta tada kan kasashen da ba su da daidaiton ra’ayi da ita.

Dimokuradiyya shi ne yadda jama’ar wata kasa ke iya gudanar da harkokinta. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, dimokuradiyya ba abin ado ba ne, abu ne da ke taimaka wa wajen daidaita matsalolin da al’umma ke fuskanta. Akwai hanyoyi da dama na wanzar da dimokuradiyya a maimakon tsarin da kasashen yamma ke bi. Yadda za a tabbatar da zaman walwalar jama’a shi ne ma’auni daya kacal na tantance tsarin dimokuradiyyar wata kasa yana da kyau ko a’a.

Abin dariya ne yadda Amurka ta kira “Taron Kolin Dimokuradiyya”_fororder_微信图片_20211210211005

A yayin da shugaba Biden ke lacca a kan batun dimokuradiyya, a wajen hedkwatar MDD da ke birnin New York, an gano wasu masu zanga-zanga dake da wani akwatin jana’iza da aka rubutawa “Dimokuradiyyar Amurka” a jikinsa, don gudanar da jana’izar dimokuradiyyar kasar. (Lubabatu)